Wasu mutum shida sun riga mu gidan gaskiya bayan kwankwadar barasa da ake zargin wani abokinsu ne ya ba su suka sha a yankin Ogbogbo na Karamar Hukumar Ijebu ta Arewa maso Gabas a Jihar Ogun.
Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne ranar Talatar da ta gabata a wata mashaya, lokacin da wasu abokai su bakwai suka hadu domin su gwangwaje.
- Tsarin raba tallafin N8,000 yaudara ce — Uba Sani
- Wata kungiya ta yi gangamin kona Al-Qur’ani a Denmark
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa dukkan mutum shidan da suka sha barasar ne suka mutu, sai na bakwai din wanda shi ne ya kawo musu, amma bai sha ba.
Tun farko dai an ce mamatan da wanda ya kawo musu giyar sun yi wata zazzafar sa-in-sa ne, amma daga bisani aka sasanta su.
Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta yi bayanin cewa daga nan ne wanda ake zargi da kisan ya yi alkawarin zai kawo musu giya a matsayin wani mataki na sasantawa.
Daga nan ne ya je gida ya dauko musu giyar, inda dukkansu suka sha, ban da shi.
Sai dai ’yan sa’o’i kadan bayan sun koma gidajensu, sai labari ya bazu cewa mutum biyu sun mutu, hudu kuma na kwance a asibiti.
Majiyar ta kuma ce kashegari ragowar mutum hudun su ma sun mutu, amma wanda ake zargin ya cika wandonsa da iska.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin, kodayake ta ki cewa uffan a kan adadin wadanda suka mutun.