Hukumomin lafiya sun tabbatar da rasuwar mutum hudu bayan karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 a Jihar Edo.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiyar Jihar Edo, Osamwonyi Irowa, ya bayyana wa taron COVID-19 a ranar Laraba cewa a cikin mutum hudun, har da wani dan kasar Amurka.
“A cikin awa 24 mun samu rahoton mutuwar mutum hudu, bayan karbar rigakafin COVID-19,” kamar yadda ya bayyana wa taron na yau da kullum a Benin, babban birin jihar.
Ya ce, “Daya daga cikin wadanda suka mutu, mai shekara 57, an yi masa allurar rigakafin Johnson & Johnson a kasar Amurka, sai dai yana dauke da ciwon siga.
“Amma hakan bai kamata ya hana mutane karbar allurar rigakafin ba, saboda wani ya mutu ba,” inji shi.
A cewar sa, an yi wa mutum 399 gwajin cutar, inda aka gano mutum 65 masu dauke da ita, kashi 19.2 cikin 100 ke nan na wadanda suka kamu da cutar a jihar.
Irowa ya bayyana cewa mutum 30 ne suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar tun bayan bullar samfurin Delta a ranar 17 ga watan Yuli.
Ya ce babu tabbacin cewa rigakafin na da tasiri dari bisa dari ga wadanda aka yi wa, sannan wadanda aka yi wa rigakafin za su iya mutuwa sakamakon cutar.
Irowa ya ja hankalin al’ummar jihar da su amince tare da karbar rigakafin don kare kansu.
“Ya kamata wadanda aka yi wa allurar rigakafin su ci gaba da bin matakan kariyar COVID-19, saboda za su iya sake kamuwa da cutar duk da cewa sun karbi rigakafin,” a cewarsa.