✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun mutu yayin tarwatsa ‘yan shi’a a Kaduna

’Yan shi’ar sun fito tattaki ne domin nuna goyon baya kan Falasɗinawan da Isra’ila ke yi wa kisan kiyashi.

Mutum huɗu ne aka ce sun rasa rayukansu a lokacin da ‘yan sanda a Kaduna suka yi harbi kan mai uwa da wabi domin tarwatsa Kungiyar IMN wadda aka fi sani da ‘yan shi’a da ke gudanar da bukukuwan ranar Kudus ta duniya.

Aminiya ta kuma samu rahoton cewa mutane 20 sun samu raunuka daban-daban a yayin da lamarin ya faru.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hasan ya tabbatar da cewa jami’an ’yan sanda uku sun jikkata kuma an kai su asibiti domin yi musu magani.

Sai dai ASP Hassan ya ƙaryata zargin cewa sun kashe ‘yan shi’a tare da cewa ba a yi amfani da harsashi  ba wajen tarwatsa masu tattakin.

Kamar yadda wakiliyarmu ta ruwaito, ’yan shi’a a wannan Juma’a sun gudanar da tattakin lumana a babban birnin jihar domin gudanar da bukukuwan ranar Ƙudus ta duniya inda jami’an tsaro suka yi yunƙurin hana su.

Aminiya ta ruwaito cewa, ‘yan Shi’an sun taru ne a kusa da Shataletalen Katsina daura da titin Ahmadu Bello kafin zuwan ‘yan sandan, inda suka yi yunƙurin tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye da dai sauransu.

Wannan lamari dai ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin, musamman waɗanda ke da sana’o’i a kan titin Ahmadu Bello, yayin da ‘yan sanda suka yi ta harbe-harbe don tarwatsa masu zanga-zangar.

Da yake bayani a wata tattauna bayan faruwar lamarin, Malam Aliyu Tirmiziy, ɗaya daga cikin shugabannin IMN ya tabbatar da mutuwar mambobinsu huɗu yayin da wasu 20 suka samu raunuka.

Ya ce, “Mun saba fitowa a ranar Juma’ar ƙarshe na kowane watan Ramadan domin mu yi zanga-zangar lumana tare da nuna goyon bayanmu ga al’ummar Falasɗinu kan cin zarafin da ake yi musu kamar yadda wasu ke yi a faɗin duniya.

“Muna gudanar da tattaki na lumana, amma a wannan karon da muke shirin farawa sai ‘yan sanda suka zo suka watsa mana hayaƙi mai sa hawaye suka fara ihu kuma ana cikin haka ne aka kashe mambobinmu huɗu yayin da 20 suka samu raunuka.”

Shi ma da yake nasa jawabin, Farfesa Dauda Nalado, ɗan ƙungiyar IMN, ya yi kira ga ɗaukacin jama’a da sauran ‘yan ƙasa da su yi Allah-wadai da kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Falasɗinu.

Bisa al’ada dai duk Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan, ’yan shi’a na gudanar da tattakin domin nuna wa al’ummar Falasdinu goyon baya dangane da irin zaluncin da kasar Isra’ila ke yi musu.