✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa Bobrisky laifin wulaƙanta naira

EFCC ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo yana yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta samu Idris Olanrewaju Okuneye da aka fi sani da Bobrisky da laifin wulaƙanta naira.

Sai dai Alƙalin kotun, Abimbola Awogboro, ya jingine yanke wa Bobrisky hukunci zuwa ranar 9 ga watan Afrilu inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC.

Kafin samunsa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.

Alƙalin ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.

Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.

“Ina da tarin mabiya fiye da miliyan biyar. Zan ɗora bidiyo a shafina kuma na faɗakar da mutane game da yin liƙi da kuɗi. Ba zan sake yi ba, na yi da na sanin abubuwan da na yi.”

Bobrisky dai na iya fuskantar hukuncin wata shida a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 50 ko ma ya yi duka biyun.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Larabar a gabata ce hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta kama Bobrisky saboda zarginsa da wulaƙanta takardun kuɗi na naira.

EFCC ta bayyana hakan ne cikin sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis.

EFCC ta bayyana cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.

Hukumar ta ce bidiyon ya naɗo Bobrisky yana watsi da takardun kuɗin a bikin nuna wani fim mai suna Ajakaju wanda jarumar Nollywood, Eniola Ajao ta shirya da aka yi ranar 24 ga watan Maris a shagon Film One Circle Mall da ke Lekki a Jihar Legas.

Sanarwar ta ce a baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.

A cewar hukumar, Bobrisky ya amsa gayyatar da ta yi masa kuma da safiyar ranar Laraba ya bayyana a ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.