Akalla mutum 32 da suka hadar sa yara 20 da manya 12 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwalekwale a garin Ibbi da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.
Kwale-kwalen na dauke da masunta sama da 50 daga garin Ibbi zuwa Gabashin jihar a ranar Asabar don yin su a yayin da ya kife a kusa da gabar kogin Benuwai.
- Dan kwallon kasar Ghana ya rasu ana tsaka da wasa
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Za A Yi In Ana So A Hana Sayen Kuri’a —Masana
Wani mazaunin garin Ibbi, Malam Ibrahim Ibbi, ya ce yara 20 da manya 12 ne suka mutu a hatsarin.
Gwamnan jihar, Agbu Kefas, ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici, kwanaki kadan bayan faruwar wani hatsarin jirgin ruwan a Karim Lamido.
Ya jajanta wa al’ummar Ibbi tare da addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu.
Gwamna Kefas, ya ce gwamnati ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike domin gano musabbabin yawan hatsarin kwalekwale a jihar.
Gwamnan ya ce nan ba da jimawa da kansa zai zagaya yankunan da abin ya shafa da nufin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ruwa.
Kazalika ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don kare rayukan al’ummar jihar.