Mutum uku sun rasu wasu 10 sun samu raunukan harbi a rikicin sojoji da direbobin baburan A Daidaita Sahu a garin Gashua, Karama Hukumar Bade ta Jihar Yobe.
A ranar Lahadi ne aka ba hamata iska bayan wata motar sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke aikin sintiri ta yi taho-mu-gama da wasu masu baburan, inda wani direban baburin da fasinjojinsa suka samu raunuka.
Hatsarin da ya auku a Gadar Gashua da ke kusa da garin ya fusata jama’ar yankin inda suke zargin sojojin da gudun wuce kima da tukin ganganci da kuma rashin bin dokar hanya.
Wani shaida ya bayyana cewa a sakamakon haka ne matasa wadanda akasarinsu masu baburan ne suka fara zanga-zanga, suka tare babban titin zuwa Gashua.
- Hajji: Maniyyatan Filato 135 Ba Za Su Samu Sauke Farali Ba
- Shugabannin bankuna na amsa tambayoyi kan Badaƙalar Beta Edu da Sadiya —EFCC
“A sakamakon haka ne sojoi suka mayar da martani ta hanyar yin harbi, har aka samu rasuwar mutum daya a wurin,” in ji shi.
Wani ganau kuma dan jarida da ya nemi sa sakaya sunansa ya ce hukumomin Asibitin Kwararru da ke Gashua sun tabbatar da rasuwar mutane uku daga cikin wadanda aka harba.
Dan jaridan ya kara da cewa wasu mutum 10 sun samu raunuka daga harbin da sojojin suka yi, yawanci a kafafunsu.
Mataimakin kakakin Rundunar Operation Hadin Kai da ke Damaturu, Kyaftin Shehu Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce suna jiran rahoton jami’insu da ke kula da yankin da abin ya faru.
Sanata Ahmad Lawan, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, ya bukaci hukumomin soji su binciki lamarin domin daukar matakin da ya dace.