Wata mata da yara biyu sun gamu da ajalinsu a lokacin da kwalekwalen da suke tafiya a cikinsa ya nitse da su a Kogin Binuwai a jihar Taraba.
Hatsarin ya auku ne garin Ibbi da ke karamar hukumar Ibbi a jihar, a lokacin da kwalekwalen mai inji ya nitse a kan hanyarsa ta zuwa garin Sarkin Kudu.
- Dukkan alamu sun nuna PDP za ta lashe Legas a 2023 — Atiku
- Rashin tsaro ya rage mana kudin shiga daga man fetur – Buhari
kwalekwalen dai na dauke da mutane masu yawa da mota lokacin da ya gamu da iftila’in.
Wani matukin kwalekwale mai suna Jalo Ibbi wanda wannan lamarin ya auku a kan idonsa ya ce kwalekwalen na dauke ne da ’yan kasuwa daga garin na Ibbi, a kan hanyarsu ta zuwa Sarkin Kudu domin cin kasuwa, inda suke nitse a tsakiyar kogi.
Ya ce wadanda suka iya iyo sun taimaka wajen ceto wasu daga cikin fasinjojin dake cikin kwalekwalen.
Jalo ya ce an gano gawar matar da yaran su biyu kuma har yanzu ana ci gaba da neman wasu gawarwaki a cikin kogin na Binuwai.
Shugaban karamar hukumar Ibbi, Mista Bako, ya tabbatar da aukuwar hatsarin kuma ya bai wa masu tuka kwalekwalen da suke sufurin jama’a a kogunan daga yanzu doke fasinjojinsu su rika sanya rigar da ke hana mutum nitsewa a ruwa wato ‘life jacket’.