Akalla mutum 27 ne suka jikkata bayan da wani sashe na ginin wani filin wasan kwallon kwando ya rufta a Cairo, babban birnin Kasar Masar, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya kasar ta sanar.
Kakakin ma’aikatar, Hossam Abdel Ghaffar, ya tabbatar da jikkatar mutum 27, inda ya kara da cewar ana fargabar wasu kumagini ya danne su.
- Buhari zai je Kogi kaddamar da ayyuka ranar Alhamis
- A karon farko, an ba Bahaushe Kwamishina a Kuros Riba
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da take nuna an samu asarar rayuka.
Tuni Hukumar Kwallon Kwando ta Kasar, ta dakatar da wasan da ake bugawa tsakanin kungiyoyin Al Ittihad ta birnin Alexandria da kuma ta Al Ahly.
An aike da akalla motocin asibiti sama da 20 zuwa filin wasan don gudanar da aikin ceto kan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ministan Matasa da Wasanni na Kasar, Ashraf Sobhi, ya kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki musabbabin faruwar lamarin.