✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun tsere bayan jirgin soji ya watsa ’yan bindiga

’Yan bindiga sun tarwatse a Dajin Rugu, mutanen da ke hannunsu suka tsere.

Mutum 20 ne suka tsere daga hannun ’yan bindiga, ciki har da mata 18, bayan jirgin soji ya fara shawagi a sararin samaniyar Dajin Rugu a Jihar Katsina.

Wani matashi daga cikin mutanen da suka kubuta ya ce da ganin jirgin na soji ya fara shawagi sai ’yan bindigar suka ranta a na kare daga maboyarsu da ke cikin dajin na Rugu.

  1. Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 13 sun kona su a Sakkwato
  2. Makarantar Bethel: An sako karin dalibai 10

“Muna zaune yaran ’yan bindigar suna gadin mu yadda suka saba, sai kawai muka ji karar jirgin soji yana shawagi. Kan ka ce wani abu sai suka fara guje-gujen neman tsira, ni kuma da na ga haka, sai na fara kokarin balla kwadon da suka daure kafata, na fara gudu,” inji matashin mai shekara 27.

Daya daga cikin wadanda suka tseren ya ce ya fada wa matan da ke tare da su a hannun masu garkuwar cewa kowaccensu ta dauko ’ya’yanta saboda duk su samu su tsira.

Mutunen da suka kubutar sun shaida wa ’yan jarida a Katsina ranar Asabar cewa watansu biyar a hannun ’yan bindiga kafin su samu su tsira a ranar Juma’a da dare.

Mutum 20 din da suka kubuta sun hada da matan aure 10 da kananan yara mata tawkas, sai wani matashi da wani saurayi.