Akalla mutane 20 ne aka gano sun kamu da cutar kuturta a jihar Kogi, sabanin ikirarin jihar na cewa babu mai dauke da ita a cikinta.
Jami’ar Kungiyar Dake Yaki da Cutar a Najeriya, Misis Hannah Fashona wacce ta tabbatar da hakan ga manema labarai a Lakwaja ta ce an sami adadin ne tsakanin watannin Janairu da Disambar 2020.
- Ya kamata a hana makiyayan kasashen waje shigowa Najeriya kiwo – Ganduje
- Duk mai COVID-19 da ya shigo Jihar Kogi zai warke —Yahaya Bello
Misis Hannah wacce ta bayyana hakan yayin rabon kayan tallafi ga masu karamin karfi a jihar ta kuma ce kungiyarsu ta lashi takobin ganin karshen cutar a Najeriya.
Ta kuma ce cibiyar da aka kafa domin kula da masu dauke da cutar a jihar dake Ochadamu ta sami nasarar yin magani ga wadansu da suka kamu da ita.
Ta ce bincike ya nuna cewa kimanin mutane miliyan uku ne ke fama da cutar a fadin duniya saboda tsoro da kuma rashin sani, yayin da take ci gaba da yin barazana ga lafiyarsu.
Jami’ar kungiyar ta ce sama da mutane 600 ne ake yi wa maganin cutar a kullum a fadin duniya, yayin da sama da rabin wadanda ke kamuwa da ita kuma yara ne kanana.
Wannan, a cewarta shine ya karfafa gwiwar kungiyarsu kuma ta dukufa bincike ba dare ba rana domin ganin ta magance cutar baki daya.
Yayin rabon dai, an raba kayan tallafi da suka hada da kayan abinci kamar shinkafa da wake da garin kwaki da taliya da man girki da kafi-zabo da sukari da gishiri da kuma kayan tsafta.