✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 sun mutu da raunata 23 a gobarar tukunyar gas a Legas

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da jikkatar akalla mutum 23 a gobarar tukunyar gas da ya…

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da jikkatar akalla mutum 23 a gobarar tukunyar gas da ya auku a ranar Alhamis a unguwar Ajegule da ke daura da Apapa a jihar Legas.

Babban Daraktan Hukumar Dakta Femi Oke-Osanyintolu, ne ya tabbatar da hakan ya ce hadarin ya faru ne sakamakon fashewar tukunyar gas da ke yoyo ya ce wutar ta yadu zuwa gidajen da ke daura da ainihin inda lamarin ya abku ne biyo bayan kiran wayar salula da wani da ba a san kowa ya yayi ba, a wajen da gobarar ta tashi.

Ya ce, zuwa yanzu ana kula da lafiyar wadanda suka jikkata a babban asibitin Gbagada da ke Legas.

Wajen da tukunyar gas ta fashe