✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 sun mutu bayan tankar gas ta yi bindiga a Ribas

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safe bayan da tankar  ta faɗi.

Aƙalla mutum biyu ne suka rasu bayan wata tankar gas, ta yi bindiga a gadar Obiri zuwa Ikwerre da ke Gabas  maso Yammacin Fatakwal a Jihar Ribas.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:25 na safe, bayan tankar  ta faɗi a lokacin da ta ke ƙoƙarin ƙetare gadar sama, inda ta yi karo da wata mota ɗauke da mutane biyu  a ciki.

Ganau ya ce, “Ofishina na kusa. Wani mummunan lamari ne ya faru. Wasu mutane biyu a cikin wata motar salon da aka ajiye a kusa da su, sun gagara gane su saboda ƙunar wuta. Tankar dai tana ƙoƙarin ƙetara gadar sama sai ta faɗi ta yi bindiga.”

Gadar sama ta Obiri zuwa Kwere na kan hanyar zuwa filin jirgin saman na Fatakwal, a Omagwa a Ƙaramar Hukumar Ikwerre.

Wani mai sunansa da Lucky, ya ce ƙarar fashewar ta bazu zuwa wuraren zaman jama’a da ke kusa da gadar sama kuma ta haifar da fargaba.

“Da misalin ƙarfe 9:00 na safe ne, na nufi jami’ar Fatakwal na ga wuta.

“Na yi saurin juyowa saboda ina tuƙi. Motoci da yawa ne suka fara sauya hanya don gujewa inda gobarar ta tashi, wasu ma har bidiyo da wayoyinsu suka riƙa ɗaukar wutar.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma tabbatar adadin waɗanda suka mutu.