✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 sun mutu a gasar shan maganin gargajiya a Kogi

Masu bajintar shan tsimi sun mutu bayan kwankwaɗar maganin gargajiyar da ake kira ‘gegemu’ da ‘obo’.

Ana fargabar cewa wasu mutum biyu daga cikin huɗu sun mutu bayan gasar shan tsimi da aka gudanar a yankin Isanlu na Karamar Hukumar Yagba ta Gabas da ke Jihar Kogi.

Aminiya ta ruwaito cewa, mutanen huɗu sun shiga gasar shan maganin gargajiyar ne da aka haɗa da sassaƙe da saiwowin tsirrai domin gwada ƙwazonsu na shan tsimi.

Sai dai an yi rashin sa’a biyu daga cikin masu gwada bajintar shan tsimin sun mutu bayan kwankwaɗar maganin gargajiyar da ake kira ‘gegemu’ da ‘obo’ a ranar Alhamis.

Wani mazaunin yankin mai suna Bidemi, ya bayyana cewa tsimin ya yi ajalin mutum biyu yayin da aka kwantar da sauran biyun a asibitin ECWA da ke Makuntu-Isanlu inda suke karɓar magani.

“Bayan wani lokaci kaɗan da shan maganin gargajiyar ne sai ɗaya daga cikinsu mai suna Okiribo ya soma ciwon ciki, kuma bayan ya zaga zai yi bayan gida a wani ɗan jeji da ke kusa sai rai ya yi masa hali yana tsugunno.

“Haka shi ma wani daga cikinsu mai suna Samuel ya soma kukan cikinsa yana murɗawa, inda bayan ya koma gida ya ce ga garinku nan.

“Bayan farfadowar Shola Pempe a gadon asibiti, sai ya labarta wa jama’a cewa ai tsimi suka kwankwaɗa .”

Kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, SP William Aya wanda Aminiya ta tuntuba, ya ce zai bincika domin samun karin bayani kan aukuwar lamarin.