✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 18 sun kone kurmus a hatsarin mota

Mutum 18 ne aka sanar sun kone kurmus a wani hatsarin mota da ya auku a ranar Lahadi tsakanin babbar hanyar Ihiala zuwa Anaca a…

Mutum 18 ne aka sanar sun kone kurmus a wani hatsarin mota da ya auku a ranar Lahadi tsakanin babbar hanyar Ihiala zuwa Anaca a Jihar Anambra.

Hatsarin ya auku ne sakamakon fashewar daya daga cikin tayoyin baya na motar inda nan take ta rika tuntsirawa sannan ta kama da wuta.

Wannan mummunan tsautsayi shi ne ya yi sanadin da daukacin fasinjojin motar suka kone kurmus.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura, Kamal Musa da ke ofishin Ihiala ya tabbatar wa Aminiya cewa, “Direban motar ya fito da gudu a yayin da daya daga cikin tayoyin motarsa ta fashe. Hakan ya sa ya tsallake rijiya da baya”.

Kamal Musa ya kara da cewa, “Mutum daya daga cikin fasinjojin da ya fito ta taga ya kone kurmus bayan nan sai ya rasu, an dai kai gawarwakinsu asibitin Laudera”.

Kwamandan ya yi kira ga direbobi su rika yin tuki cikin natsuwa tare da kiyayen dokokin sufuri.