✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano

An kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar yau Laraba, inda ya haɗa wata babbar mota ƙirar DAF da babur ƙirar Jincheng.

Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce tuƙin ganganci ne ya haddasa hatsarin.

“Daga cikin mutum shida da hatsarin ya shafa, biyu sun rasu, yayin da ɗaya ya samu munanan raunuka,” in ji shi.

Jami’an FRSC sun isa wajen da hatsarin ya auku cikin minti uku sannan suka kai wanda ya jikkata zuwa Asibitin Murtala Muhammad domin samun kulawar gaggawa.

An kuma kai gawarwakin waɗanda suka rasu Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

An miƙa motocin da sauran kayayyakin da aka ƙwato zuwa ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa domin ci gaba da bincike.

FRSC, ta shawarci direbobi da su bi dokokin hanya tare da yin tuƙi cikin taka-tsantsan don kaucewa irin waɗannan haɗura.