Wani jirgin kasa mai dauke da kananan yara da matasa, wadanda adadinsu ya kai akalla 50, ya kauce hanya ya fada cikin wani kogi a kasar Austria.
Kwamandan masu ba da agajin gaggawa na birnin Salzburg, Anton Schilcher, ya ce mutum 17 ne suka yi rauni a hatsarin a ranar Juma’a.
Hatsarin ya faru ne ‘yan mintuna kadan bayan karfe 7:00 na safiyar Juma’a (karfe 6.00 ke nan agogon Najeriya) kusa da Kendlbruck.
An rawaito cewa jirgin kasar ya nutse kimanin mita hudu a cikin kogin.
A cewar kwamnadan masu aikin ceton, an rufe layukan dogo bayan faruwar lamarin har zuwa nan da wani lokaci.
An bayyana cewa jirgin na dauke da mutum 50 a lokacin da ya tsunduma cikin kogin.
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ma ta kai dauki wajen, inda ta bayyana cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa yankin Tamsweg.
Tamsweg wani wuri ne na musamman da yara da ‘yan makaranta ke zuwa yawon bude ido a lokuta daban-daban.