Kimanin mutane 15 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan wani jirgin kasa mai daukar kaya ya yi taho-mu-gama da wani na fasinja a kasar Indiya.
A safiyar Litinin ne jirgin dakon kaya ya yi taho-mu-gama da jirgin fasinjan kamfanin Kanchanjunga Express a gundumar Darjeeling da ke Jihar Bengal ta Yamma.
Wani babban jami’in ’yan sanda a gundumar Darjeeling, Abhishek Roy, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, an zakulo gawarwaki sama da 15 daga cikin jiragen kasan.
Roy ya kara da cewa, kusan mutane 30 ne suka jikkata, amma masu aikin ceto da likitoci suna ci gaba da aiki a yayin da mazauna yankin da jami’an agaji ke kokarin kawar da tarkacen jiragen kasan da abin ya shafa.
- Saudiyya ta kayyade wa alhazai lokacin jifa saboda tsananin zafi
- Al’ummar Jamus sun raba shanun layya 700 a Kano
Kakakin hukumar jiragen kasa a yankin arewa maso gabashin kasar, Sabyasachi De, ya ce uku daga cikin wadanda suka mutu ma’aikatan jirgin kasa ne.
Babban Ministan West Bengal, Mamata Banerjee, ya ce, an tura likitoci, motocin daukar marasa lafiya da jami’an agaji zuwa wurin da hadarin ya afku, wanda ke kusa kusa da tashar New Jalpaiguri.
Rahotannin farko dai sun nuna cewa kuskuren dan Adam ne ya haddasa hatsarin jiragen kasan.
Layukan dogon kasar Indiya da ke yawan jigilar jama’a suna yawan samun haddura a kowace shekara.