An samu rahoton bullar cutar zazzabin Lassa a Jihar Taraba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 14 cikin watanni uku da suka gabata.
Hakazalika, an yi wa mutum 84 gwajin cutar, tare da tabbatar da mutum 33 da suka kamu da cuta.
- Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN
- Mayaƙan Lakurawa 3 sun shiga hannu kan bayar da cin hancin N1.6m
Shugaban Sashen Ayyukan Asibiti na Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya (FMC), da ke Jalingo, Dokta Kuni Joseph ne, ya bayyana wannan alkaluma.
Ya ce mutum shida daga cikin wadanda suka mutu, sun rasu ne a makon da ya gabata.
Ya kara da cewa, daga ranar 24 ga watan Oktoba, 2024 zuwa watan Janairu 2025, an samu rahoton mutum 84 da ake zargi sun kamu da cutar.
Daga cikin su, mutum tara sun samu sauki kuma an sallame su, yayin da mutum shida har yanzu suna samun kulawa.
“Wannan shi ne karo na farko da muka samu alkaluma masu yawa na cutar a Jihar Taraba,” in ji Dokta Joseph.
Ya ce FMC Jalingo na aiki tare da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), domin dakile cutar.
Dokta Joseph, ya tabbatar wa al’umma cewa FMC Jalingo na da duk kayan aikin da ake bukata don kula da masu fama da cutar.
Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu lura tare da kare kansu, musamman a bangaren kiwon lafiya.