Sakamakon matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya, akalla mutum 14 ake kashewa kullum a yankin Arewa baya ga rayuka 8,372 da aka hallaka a yankin a 2021, injin Kungiyar Masu Kafafen Yada Labarai a Arewa (NBMOA).
Kungiyar ta ce a halin da ake ciki, kananan yara da ba su zuwa makaranta a Najeriya sun kai miliyan 10.5, yayin da kasar ke da ’yan gudun hijira miliyan 2.7, adadi mafi girma a Afirka.
- Aisha Buhari ta yada bidiyon zargin sojoji da taimakon ’yan bindigar Zamfara
- Yadda aka sace Dala 50,000 a Hedikwatar APC a Abuja
Wadannan bayanai sun fito ne daga bakin shugaban riko na NBMOA, Abdullahi Yelwa, yayin tattaunawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Yelwa ya ce, kimanin kashi 21.4 cikin 100 na ’yan Najeriya suka yi fama da yunwa tsakanin 2018 zuwa 2020.
Daga nan, ya ce sun gayyaci daukacin ’yan takara masu neman mukamai a tsakanin duka jam’iyyu su fito su bayyana tsare-tsarensu wajen ceto Najeriya daga halin da tsinci kanta.
Saboda a cewarsa, “A Arewa, kullum ake fuskantar kalubale, kama daga matsalar ’yan fashin daji, ta’addanci, ’yan gudun hijira, shaye-shaye, talauci, yaran da ba su zuwa makaranta, rashin aiki ga matasa, barace-barace zuwa barazanar yunwa.
“Wadannan su ne matsalolin da ya kamata a maida hankali wajen magancewa; don haka dole duk wani dan takara mai neman kuri’ar ’yan Arewa ya daura niyar ganin bayan wadannan matsaloli.”
Da yake karin haske, Yelwa ya ce akalla mutum 8372 ne suka rasu a 2021 sakamakon matsalar tsaro, inda kimanin mutum 14 ke rasuwa a kowace rana a yankin Arewa.
“Tsakanin 2018 zuwa 2020, akalla kashi 21.4% na ’yan Najeriya ne suka yi fama da yunwa, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 14.4% na ’yan kasar na yin shaye-shaye.
“Sannan ana da kananan yara miliyan 10.5 da ba su halartar makaranta, wato daya cikin kowadanne yara baiyar a Najeriya.
“Rashin aiki ga matasa ya kai kashi 17.69 cikin 100 a 2019, yayin da ake da ’yan gudun hijira da rikici ya daidaita mutum miliyan 2.7.”