Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an.
- Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe
- Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati
“A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi.
“Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take.
“Suna cikin guje mana ne a cikin motar da suka sace ƙirar Toyota Camry suka yi haɗari a babban titin Abuja-Keffi.
“Jami’anmu da ke ofishin ‘yan sanda na Goshen ne suka kwashe su zuwa asibiti, a nan mutum huɗu suka mutu.
“Ɗayan da ya rage kuma na hannunmu likitoci na bashi kulawa.
Binciken ‘yan sanda dai ya kai ga gano wasu kayan da ‘yan fashin suka sata da suka haɗa wayoyin hannu 12, agogunan hannu, sai makamai da suka haɗa da manyan wuƙaƙe biyu, sukundireba, da kuma layu.