✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 120 sun kwanta jinya bayan shakar gurbatacciyar iska a Kano

Wani ne ya fasa wata tukunyar gas mai dauke da sinadarin guba.

Akalla mutane 120 aka kwantar a asibiti sakamakon shakar wata gurbatacciyar iskar da ta mamaye unguwar Mundadu daga wata tukunyar gas da ta fashe.

Majiyoyi sun danganta matsalar da fasa tukunyar da ke dauke da gas din da wani mutum mai tattara karafa yayi lokacin da yake aiki a kansu.

Mazauna yankin sun ce iskar da ta fita daga tukunyar ta gurbata yankin, abinda ya sa ta haifar da sarkewar numfashi, kamar yadda Mai anguwar yankin Magaji Abdullahi ya tabbatar.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an kai mutane da dama asibitoci daban daban domin kula da lafiyar su.

Abdullahi ya ce an kai mutane kusan 70 Cibiyar Kula da Lafiya da ke Jaen, yayin da aka kai 50 Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed.

Sai dai jami’in ya ce kawo yanzu babu wanda ya rasa ransa sakamakon hadarin.

“Kimanin mutum 70 daga cikinsu an kai su Cibiyar Kula da Lafiya  ta Unguwar Jaen, yayin da 50 kuma aka kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin yi musu magani,” inji Saminu.

Aminiya ta lura cewa galibin wadanda lamarin ya shafa mata ne da kananan yara.