✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 12 sun mutu a turmutsitsin wurin ibada a Indiya

Bayanai sun ce an tabbatar da jikkatar mutum 13.

Akalla mutum 12 ne suka rasu, da dama kuma suka samu raunuka a yayin wani turmutsitsi da ya faru wajen bautar addinin Hindu na Mata Vaishno Devi.

Bayanai sun ce dimbin masu bauta ne suka rika tururuwar hallara a wurin abin bautarsu a ranar farko ta sabuwar shekara.

Dubban mutane ne ke zuwa wurin butar a kullum inda ake kyautata zaton sakamakon hutun da ake yi, an samu karuwar masu kai ziyara.

Cikin gaggawa aka fara aikin ceto a wurin bautar na Vaishno Devi mai tazarar kilomita 60 da garin Jammu, lamarin da ya sanya aka dakatar da masu bautar daga bisani kuma aka ba su dama su ci gaba.

Wasu bayanai sun ce an tabbatar da mutum 13 sun samu raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Wani jami’in ya kuma ce akwai yiwuwar za a iya samun karuwar mace-mace ganin yadda mutane ke kara tururuwa zuwa wurin bautar.

Wannan wurin bautar da ake kira Holy Cave Shrine na kusa ne da garin Katra; kuma yana daya daga cikin wuraren ibada mafiya daraja da masu ziyarar ibada ke zuwa a kasar ta Indiya.

Akwai miliyoyin wuraren bauta na mabiya addinin Hindu a Indiya a lunguna da sako na birane, garuruwa da kuma kauyuka ciki har da yankunan Himalayas da wasu dazukan a Kudancin kasar.

Gabanin barkewar annobar Coronavirus, ana samun akalla mutum dubu 100 da ke tattaki ta ziririn wasu koguna da ke kai wa zuwa ga wurin bautar.

Muhukunta sun bayyana cewa akwai kimanin mutum 25,000 da ke zuwa wurin bautar duk rana, inda wasu rahotannin suka adadin wadanda ke zuwa na zarta hakan a wasu lokutan.

Irin wannan ibtila’i na tirmitsitsi a wurin bauta da suka auku karo biyu a shekarar 2008 sun yi ajalin sama da mabiya addinin Hindu 370 a kasar Indiya.

Akwai kuma wadanda suka auku a Kerala a shekarar 2011 da kuma Madhya Pradesh shekaru biyu baya wanda kowannensu ya yi sanadiyar rayukan fiye da mutum 100.