Mutanen da suka rasu a sakamakon bude wuta da ’yan bindiga suka yi a yankin Pinau da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato sun karu zuwa mutum 11.
- Gwamnati za ta kara kudaden haraji a 2022 —Ministar Kudi
- Ba a Najeriya ne kawai ake fuskantar kashe-kashe ba – Fadar Shugaban Kasa
Daga bayan wani shugaban matasan yankin, Shafi’i Sambo, ya ce, “Yanzu mutum 11 ne suka rasu, takwas daga cikinsu maza ne, sai kuma mata da kanana yara.”
’Yan bindiga sun far wa kasuwar da ke unguwar Pinau da ka Karamar Hukumar Wase ta Jihar ne ranar Lahadi.
Gabanin harin, a ranar Laraba 8 ga Disamba, 2021, mazauna wasu kauyuka a karamar hukumar sun yi korafin cewa ’yan bindiga na shigar yankunansu.
Sun kuma koka cewa masu hada baki da ’yan bindigar suna kawo cikas ga kokarin jami’an tsaro na magance matsalar.
Majiyar ta ce, “Miliyoyi suke karba a matsayin kudin fansa, wani lokacin Naira miliyan biyu, har zuwa miliyan biyar. Kwana uku da suka wuce sun karbi Naira miliyan biyar kafin suka sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi.”
Wakilinmu a Jos ya nemi kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, domin samun karin bayani, sai dai jami’in dan sandan bai amsa kiran wayan wakilin namu ko rubutaccen sakon da ya tura mishi ba.
An kai harin ne kwanaki kadan bayan wani kisan gilla da ’yan bindiga suka yi wa wasu matafiya da suka tare suka kuma sa musu wuta a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.