Daya daga cikin ‘yan bindigar da suka kai hari Unguwar Bulus da Unguwar Gimbiya a Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna, ya yi gamo da karshensa a hannun mutanen gari.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa mutum uku daga yankunan sun rasa rayukansu yayin harin da ’yan bindigar suka kai da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis.
- Majalisar Wakilai za ta tsunduma yajin aiki saboda matsalar tsaro
- NAJERIYA A YAU: Yadda sakacin hukumomin tsaron Najeriya ya hallaka jama’a da dama
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shafe tsawon awanni suna harbe-harbe, lamarin da ya sanya mutane da dama suka ranta a na kare.
Wani mazaunin yankin da aka kashe masa dan uwa a yayin harin, ya ce a halin yanzu suna cikin firgici da damuwa.
Ben Maigari ya ce ‘yan bindigar sun kashe wani yaron dan uwansa sannan suka sace mahaifinsa a yayin harin da suka kai Unguwar Bulus.
“Mun jiyo karar harbin bindiga tun kafin dare ya raba don mutane da yawa ba su kwanta ba.
“Sai bayan komai ya lafa muka samu labarin sun kashe yaron dan uwana sannan sun yi awon gaba da mahaifinsa.
“Wasu mutum biyu ma sun rasa rayukansu, amma jama’a sun kashe dan bindiga daya,” a cewar Ben.
Kazalika ya ce za a birne matashin a ranar Juma’a a yankin.
Kazalika, Aminiya ta samu daga majiyar cewa da bindigar da ya riga mu gidan gaskiya an harbe shi ne a goshi.
Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ci tura sakamakon rashin amsa wayarsa.