Mazauna ƙauyen Rugar Sojidi da ke unguwar Fulani a ƙaramar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, sun kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar da suka zo sace mutanen garin.
Rahotanni sun bayyana cewar maharan sun yi garkuwa da mutum uku daga yankin kafin mutanen ƙauyen kai ɗauki.
- Jabun Kayayyaki: NAFDAC ta rufe shaguna 100 a Enugu
- Gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin Ilimi ba — Minista
A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya fitar, ya ce an kuɓutar da dukkanin mutanen uku da maharan suka sace.
Ya bayyana cewar jami’an ’yan sanda na Jere sun samu bayanan sirri daga wata majiya kan harin ’yan bindigar.
“Bayan samun labarin, ba tare da ɓata lokaci ba aka tura tawagar ‘yan sanda zuwa yankin. Da isar su, an gano cewa mazauna yankin sun yi ta maza sun ƙi yarda maharan su sace mutane kuma har sun yi nasara kashe ɗaya daga cikinsu.
“An kwato bindiga ƙirar AK-47 da alburusai shida a wane . An kuɓutar da dukkanin waɗanda aka sace ba tare da sun ji wani rauni ba,” in ji shi.
ASP Hassan, ya ce rundunar ta yi wa dajin da ke kusa da yankin ƙawanya domin cafke waɗanda suka tsere.
Kazalika, a ranar da misalin ƙarfe 1:30 na dare tawagar ’yan sandan yankin Makarfi tare da haɗin gwiwar ’yan banga na yankin sun yi nasarar daƙile wani fashi da makami a hanyar Kano zuwa Zariya.
Ya ce tawagar ta yi kaciɓis da ’yan fashi da makami, waɗanda ake zargin ɓarayin shanu ne sun tare hanyar da duwatsu.
Ya ce jami’an sun yi arangama da ɓarayin na tsawon lokaci, inda daga bisani suka tsere suka bar motarsa ƙirar Gulf mai lamba APP 166 DG.
Ya ce ba tare da ɓata lokaci ba suka sake buɗe hanyar tare da bai wa masu ababen hawa damar ci gaba da zirga-zirga.