Alhaji Musa danbade shi ne mawakin da suka samu sabani da marigayi Mamman Shata a kusan karshen rayuwar Shatan. Ya fadi yadda suka yi mutunci da kuma yadda suka samu sabani da yadda ya yi masa wakar ta’aziya bayan rasuwarsa:
Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Musa danbade: Suna na Musa danbade kuma ban san hakikanin shekaruna ba. Yadda aka yi na samu suna danbade shi ne lokacin ubangidana Ahmadu Makadin Gangar Kokuwa, Baguddure ne mutumin Gamawa, a yaransa masu suna Musa mu uku ne ba mu da inkiya, to in maigida ya ce Musa duk sai mu waigo, sai wani ya ce wannan a ce masa Musa Teri, wannan Musa danborno ni kuma Musa danbade. Ni mutumin Bade ne a Gashuwa ta Jihar Yobe.
Aminiya: Yaya aka yi kake yin waka da Hausa maimakon da yarenka?
Musa danbade: Saboda muna tare da Hausawa a Makarantar Allo a kofar gidan mahaifinmu wurin Malam Musa ’Yandoma Katsina.
Aminiya: To yaya aka yi ka fara waka?
Musa danbade: Bayan iyaye sun mutu sai na koma wurin dangin uwa a wani gari da ake ce masa Jawa. Daga Gaidam muka bi a kasa har kasar Chadi lokacin ina da shekara 15. A wannan lokacin ruwa na tafkin Chadi yana kaiwa har Malam-Fatori. Muka wuce har Tarmuwa da Damasak da garin Difa na kasar Nijar da dai sauransu. A Malam-Fatori muka shiga jirgin ruwa har Duguri daga nan muka dangana da Jammaina hedikwatar kasar Chadi. Daga nan muka bi ta Mubi, muka dangana da Kamaru. Wani ikon Allah shi ne mun tafi ina yaro da za mu dawo sai abokaina suka zama yarana bayan mun samu sabani da Ahmadu Makadin-Kokuwa, sai na ware da wani abokina mai suna dahiru. A garin Mubi ne na ziyarci yayana wanda yake da dammara yana aikin soja a garin, sunansa Isa Sa’idu. A lokacin ko noma ba na yi, ’yan wasan kokuwa ke yi mini noma. In an shirya za a yi wasan kokuwa sai a gayyace ni, in je. A zamanin mulkin Janar Yakubu Gowon na fara waka.
Aminiya: Yaushe ka jefar da kidan kokuwa ka tsiri waka da kalangu?
Musa danbade: A lokacin mulkin Shugaba Shehu Shagari na Jam’iyyar NPN na fara. Dalili kuma ina son wakar Mammalo Shata. A garin Dambam da ke Jihar Bauchi, wani Malam Ada ya ce in rika bin su, aka ban karamar lasifika. Wasu wakokin in yi nawa, wasu in yi na Mammalo Shata.
Aminiya: Yaushe kuka fara haduwa da maigidanka Mammalo Shata?
Musa danbade: A lokacin nadin Sarkin Misau, Alhaji Muhammadu Manga muka yi haduwar farko da ta karshe. Na je na gaishe shi, shi bai san ni ba, amma ni na san shi. Kafin in zo Kaduna ya rasu a 1986. Ina wasa sai maragayi Wazirin danduna suka zo suna kallona ina wasa a kofar gidan Alhaji A.D. Rufa’i a Misau, sai Wazirin danduna ya ce yaro in Allah Ya ba ka dama ka nufi yamma, don za a yi tsiya da kai.
Wani abin mamaki sai ’yan kokuwa suka ce in kai su garin Jos wasa. Don idan kokuwa ta kai kokuwa sai an nemo ni. Idan an gama kokuwa sai in kafa wasa na kidan kalangu.
Aminiya: Yaya aka yi Alhaji Sasuwai makadin Mamman Shata ya dawo yi maka kida?
Musa danbade: Shi Alhaji Sasuwai shahararren makadin kalangu ne. Bayan da aka ba da shi ga Mamman Shata don ya yi masa kida, bayan lokaci sai suka bata. Sannan ya yi wa Mammalo Shata kida da ya rasu sai ya koma garin Jos. Da na zo ina wasa, sai wani ya je ya ce masa da ana mutuwa ana dadowa da sai ya ce Mammalo Shata ya dawo. Ya ce wa Sasuwai ga wani can yana wasa kamar Mammalo Shata. A kofar gidan Mairo Habuja ya zo ya ga ina wasa, sai ya fashe da kuka. Sai yaran mahauta suka ce ba kuka zai yi ba, ya karbi kalangu. Daga nan sai ya karbi kalangu muka ci gaba da sana’armu ta kida da waka.
Aminiya: An ce yaran danlami Nasarawa ma sun koma suna bin ka, yaya aka yi?
Musa danbade: danlami Nasarawa aminina ne, wata rana da bai ji dadin jikinsa ba sai yaransa suka dawo wurina suka dafa min lokacin ana wasannin otel. Muna nan a garin Jos sai Alhaji Bature Sarkin Magana ya zo Jos, sai Sasuwai ya ce mu yi waka a kai wa Alhaji Bature. Da aka kai masa ya ji sai ya fashe da kuka. Ya ce muna ganin Mammalo ya mutu ashe bai mutu ba. Ai aiki ya same mu, sai ya ce a je Kaduna a dauki wakar a gidan rediyo. Da aka sa waka sai masoya Mammalo Shata suka yi ta murna.
Aminiya: Wane ne Mammalo Shata?
Musa danbade: Shi mutumin garin danhassan ne da ke Jihar Kano. Mahaifinsa ya yi limancin garin, sannan kuma wan Mammalo Shata shi ma ya yi limamin garin. Shi kuma ga yadda yake. Sunansa na yanka Muhammadu Tasi’u.
Aminiya: Mene alakarsu da Mamman Shata?
Musa danbade: Yana da makada da ’yan amshinsa. Idan an hadu a wasa, sai ya fito a matsayin yaron Shata.
Aminiya: Shin da gaske ka auri ’yar Mammalo Shata?
Musa danbade: Dalilin zuwa gaida iyalansa ya sa na ga ’yarsa har na neme ta sannan muka yi aure. Sunanta Salamatu, kuma a yanzu tana gidana, ’ya’yanmu 10 da ita.
Aminiya: Me ya kawo sabani tsakaninka da Mamman Shata?
Musa danbade: Allah Ya ce Wala-Tajasssu, ma’ana, babu bincike don haka ba zan fadi dalilin ba. Amma a gaban Baba Jafaru a gidan rediyo aka fara fadar. Ko kuma in ce su suka assasa fadar. Da na ce zan dauki fansa, sai aka ce za a kashe ni. Don kamar mutum ne ya mallaki kashi casa’in cikin dari, sai ya ce wani ba zai mallaki kashi goma ba. Don haka na ce duk abin da za a yi, a yi, amma ba zan fadi sauran ba. Shata ubangidana ne, ana mutunci kafin aka yi baran-baran.
Aminiya: Wacce waka kake jin ta fitar da kai?
Musa danbade: Suna da yawa, ina yin tawa, kuma ina yin ta Mamman Shata. Domin kamar yadda Mamman Shata ya rasu, idan wani ya zo in ya yi Bakandamiyar Shata, to duk mai son sa sai ya so shi. To haka na yi masoyan Mammalo suka so ni.
Aminiya: Wace waka ce Bakandamiyarka?
Musa danbade: Sai dai in ce wacce aka fi sani da ita, wakar ita ce ta Mai Tafarnuwa. Kuma wannan waka ce da aka mayar da martani da ita ga Mamman Shata don na ce ba mai kisa, ba mai rayawa in ba Allah ba.
Aminiya: Me kake nufi da Mai Tafarnuwa?
Musa danbade: Wakar Alin Kofa ce. Muna Legas inda aka gayyaci Shata da don ya yi wasa a Agege na ’Yan Kulob. Ni kuma zan yi wasa a Iddo Gada. Sai aka ce ga Mamman Shata ga Musa danbade. Dole a dage daya don a yi daya. Ka san su mutanen Legas kansu a hade yake, ba sa son rigima. Aka ce Shata shi ne babba ya yi gobe, ni in yi yau. Da na fara wasa sai sankira ya yi masa shela ya ce eh, eh, sai ya ce “Musa danbade a duniya ba wanda nake so kamar kai. Ina da Naira Talatin, na biya Naira biyar kudin mota daga Alabar Rago zuwa Iddo, kuma zan biya Naira biyar kudin komawa. Ba ni da abin da zan ba ka, amma ga Naira 20 na ba ka. Sunana Alin Kofa.”
Ana haka sai ga yaran Shata sun shigo, suka tsuguna suka gaishe ni da Alhaji Ya’u Wazirin Shata da Barrah da sauransu. Da suka koma gefe suka zauna sai na tuna da rikicinmu da Shata, na kuma hakikance cewa Shata na kusa yana ji. Sai na tashi na ba ’yan amshi waka na ce:
“Mai Tafarnuwa Alin Kofa.”
“Malam in kai Yaro ne, ai ni ko rarrafen ban fara ba.”
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa.
“Duk wanda ya zo kallon teku inba ran Lahadi ba, bai ga ruwa na juyi ba.”
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa.
Duk wanda ya ce yana kashewa, don me ubansa ya mutu bai tada ba”
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa
“Duk wanda ya ce yana kashewa don me uwarsa ta mutu bai tada ba,
Ai ba mai kashewa in ba Allah ba”
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa
“Ba mai rayawa in ba Allah ba,
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa “
Ban da jahilai karyar jama’a wa ke kisa idan ba Allah ba
“Shi zai kashe ka, shi zai raya ka.”
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa.”
“Allah kadai ke kisa, ke raya wa.
…Mai Tafarnuwa Alin Kofa.”
Aminiya: Shin an sulhunta ku?
Musa danbade: Marigayi Tsoho Abdullahi Zariya ya taba kira ta. An so an hada mu sai na ce ba zan janye kalmar da na fada ba. Na ce idan ana son mu sulhunta sai Mamman Shata ya janye cewa ba ya kisa, sai zaman ta watse.
Aminiya: Yaya ka ji da ka samu labarin rasuwarsa?
Musa danbade: Ni na fara yi misa ta’aziyya. Saboda ni ban dauki abin addini ba. Ta duniya ta kare don shi ya mutu. Na san ba zai dawo ba, kuma tasa ta yi kyau, don ni ban san yadda tawa za ta zo ba.
Aminiya: Akwai yaran Mammalo da ya gaje shi ?
Musa danbade: A’a
Aminiya: Kuma ko kai kana da magaji?
Musa danbade: A’a.