Al’ummar unguwar Vom da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato sun yi taron dangi sun hana sojoji tsare wani dan unguwar da ke kera bindigogi da kuma fasakwaurin makamai.
Mutanen sun tare hanya ne bayan sun hangi motocin sojoji daga rundunar Operation Safe Haven suna kokarin shiga unguwar da ke yankin Vwang domin tsare wanda ake zargin.
- Kotu ta sake ba da umarnin cafke Dan Sarauniya
- Yadda bulala ta sa na tsere daga makarantar allo —Obasanjo
Kakarin rundunar, Manjo Ishaku Takwa, ya ce, “Bayan samun kwararan bayanai, dakarun Operation Safe Haven sun fito da safiyar Asabar 12 ga Maris, 2022 domin tsare wani mai fasakwaurin makamai da kuma kera bindigogi a unguwar Vom da ke yankin Vwang a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
“Amma abin takaici, da mutanen unguwar suka ga jami’an tsaro sai suka fito kwansu da kwarkwata suka tare hanyar shiga unugwar, suka hana jami’an tsaro shiga unguwar su gudanar da aikin da doka ta ba su.
“Duk kokarin da aka yi na shawo kan mutanen ya ci tura; Haka kawai suka yi ta jifan jami’an tsaro da miyagun makamai, amma jami’an tsaron suka kai zuciya nesa.
“Domin guje wa kazancewar al’amarin, kwamandan rundunar, Manjo-Janar Ibrahim Ali ya umarci jami’an tsaron su janye daga yankin,” inji shi.
Operation Safe Haven rundunar hadin gwiwa ce da ke aikin samar da tsaro da zaman lafiya ne a jihohin Filato, Bauchi da kuma Kaduna.
Rundunar ta yi tir da yadda mutanen unguwar ta Vom suka hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu, tare da jan hankali mazauna game da hadarin ba wa bata-gari mafaka ko hana jami’an tsaro tsare su.
Duk da haka, sanarwar da rudunar ta ce, “Ku kwana da sanin cewa sai mun kama duk wani wanda ake zargi da aikata miyagun laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar jihar ko kasa baki daya.”