Daga Hudubar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Husain
Masallacin Sharif Ibrahim Saleh, Gwange, Maiduguri
Domin haka ne nake kira ga yin adalci. Hakika na fadi a wani taro da aka yi a Kaduna, wanda Shugaban Najeriya na yanzu ya halarta, kusan dukkan shugabanni suka halarta kuma malamai masu yawa suka halarta cewa mulki na Allah, Yana bayar da shi ga Wanda Ya so. “Ka ce: “Ya Allah Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Kake so, Kana zare mulki daga wanda Kake so, kuma Kana buwayar da wanda Kake so, kuma Kana kaskantar da wanda Kake so, ga hannunKa alheri yake. Lallai ne Kai, a kan kowane abu Mai ikon yi ne.” (k:3:26).
Na ce musu, idan Allah Ya tabbatar da wannan, to, muna karbar kaddararSa da hukuncinSa cikin cikakkiyar yarda. Sai dai a yayin da muke yarda da hukuncinSa, ba zai lizimce mu mu yarda da wasu abubuwan da suka saba wa abin da muke sa rai ba, ko abin da ya saba wa manufofinmu ba. Kuma a tare da haka wanda yake shugabancin kasar nan ya wajaba a kansa ya kiyaye wasu al’amura ba tare da lura da kasancewarsa dan Arewa ko dan Kudu ba, Musulmi ko ba Musulmi ba.
Na farko: Ba makawa ya tabbatar da zaman lafiya. Ba makawa ya himmantu ga batun zaman lafiyar kasar nan da aminci ga addini da samar da aminci ga rayuka da aminci ga hankula da aminci ga nasaba da aminci ga dukiya da abinci ga muhallin da mutane suke rayuwa.
Na biyu: Babu makawa wajen tabbatar da adalci mudalaki a tsakanin dukkan mutanen kasar nan. Adalci shi ne gishiki ga kowane mai mulki. Idan babu adalci ba za a samu zaman lafiya ba, ba za a samu ci gaba da bunkasa ko daukaka kasa ba.
Na uku: Muka ce babu makawa a rika samun daidaito a tsakanin mutane a cikin mu’amala da hakkoki. Wannan kasa Allah Madaukaki Ya ba ta albarkatu masu yawa da za su iya biyan bukatun daukacin al’ummarta. Amma muna ganin yadda kasar nan take fama da wahalar rashin ruwa da wutar lantarki da karancin magunguna da tabarbarewar ilimi da karancin komai har zuwa mafi karancin abin da dan Adam yake bukata na yau da kullum.
Ba wai muna bukatar motocin shiga na alfarma ko jiragen sama ko kumbo ba ne. A’a muna bukatar abin da dan Adam bukata ne don ya rayu.
Na hudu: Sa’annan na ce: Wannan kasa –dukkanmu – muna ganin abubuwan da suka wajaba a kanmu mu guje su, barnar da ta fi su, ita ce almundahana sai barnar siyasa da barnar masu mulki da fasadin zamantakewa da barnar a fagen tattalin arziki, har ta kai mu ga fasadi da barna sun shafi kowane bangare na hukunci. Domin haka babu shakka kowane Musulmi ko kowane mutum mai hankali a wannan kasa ya gano cewa bangarori uku da suke tafiyar da mulkin kasar nan bangaren shari’a da na majalisa da na zartarwa dukkansu wadanan masu fasadi ke juya su. Wadannan masu fasadi ba su ne dukkan mutanen kasa ba, a’a wasu ’yan kalilan din jama’a ne sanannu, amma suna ta watsa fasadi a cikin kasa.
Domin haka duk wanda yake ko zai mulki kasar nan, idan yana son samar da cikakkiyar zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasa, kuma idan yana son yana nufin ya yi amfani da mulkinsa a wannan kasa wajen samun yardar jama’a, to wajibi ne a kansa ya bi wadannan hanyoyi, kuma ya yi aiki sosai domin yin gyara:
Ya ku ’yan uwa! A yau muna ganin ’yan uwanmu a kasashen Larabawa da dama suna bin wata hanya da ta fara bayyana a ’yan kwanakin nan, ta shafi kasashe da dama da suka hada da Aljeriya da Tunisiya da Libya da Masar sun ja daga a Masar da Siriya da Yamen da Iraki inda suka ja daga a Iraki ta shafi Sudan da Afghanistan da Pakistan da wasu kasashen da makiya Musulunci suke nufin wargaza su ta hanyar kawar da shugabannin da suke gadon mulki a yanzu. Sun tashi haikan domin raunana karfin kasashen, sannan sai su kafa mulkin da za a rika zubar da jini, ko su dora shugabannin je-ka-na-yi ka. Idan suka samu nasarar haka sai kuma su gusa zuwa ga manufa ta biyu, ita ce ta gutsuttsura wadannan kasashe zuwa kananan kasashe, sun riga sun yi isharar gutsttura kasashen Musulmi zuwa kasashe da dama. Misali suna son raba kasar Sudan zuwa kasa hudu, Masar hudu, Saudiyya kasa biyu, Yamen kasa biyu Iraki uku, Najeriya kasa hudu, Chadi kasa biyu da sauransu.
Wannan shiri yana nan, kuma akwai wani shiri da aka sanya wa hannu da aka shirya a kasar Chadi, kuma wadanda suka shirya shi su ne: Amurka da Faransa da Birtaniya da wasu manya daga Afirka. Wadannan abubuwa dukkansu suna aukuwa amma mu ba mu sani ba. Muna ta barci har da minshari ba mu sani ba! Shin me suke nufi da mu?
Wadannan kasashe da sukia jarraba haka a Iraki suka ga wannan hanya ba za ta cimma nasara ba, sai suka koma ga wata hanyar, ita ce a yi amfani da ’ya’yan kowace kasa a kawo sauyi ko juyi da hannun ’ya’yanta. Wannan sauyi ko juyi wajibi ne ya gudana ta hannun ’ya’yan kasar, sai dai a taimaka musu a nuna musu yadda za su cimma haka a horar da su har ma a ba su albarkatun da suke nema! Wannan shi ne abin da yake gudana a yanzu.
Mu a nan Najeriya wasu bayanai na kungiyar Leken Asiri ta Amurka (CIA), sun tabbatar da cewa daga farkon shekarar 2011 zuwa 2015 Najeriya za ta wargaje ta rarrabu. Wadannan bayanai suna nan, kuma manyan kasar nan sun san su. Wasunsu bayan abin da ya biyo zaben da ya gabata sun bayyana cewa Amurka tana burin rarrabuwarmu. Amma mu muna gani – kuma da fatar – wannan rarrabuwa da wargajewa su same ta kafin su samu Najeriya.
Koma yaya ne ya ku ’yan uwa muminai! Wajibi ne a kanmu mu fahimci cewa lallai, mun gaza kan hakkin kanmu, mun gaza kan hakkin addininmu, mun gaza kan hakkin kasarmu. Me ya sa ku samari ba za ku hadu ku binciki wadannan al’amura ba, ko gano gaskiyar wadannan labarai ko kulle-kulle domin ko kare kanku ku kare addininku ku kare kasarku. Domin kasarku kasa ce ta al’ummar Musulmi, saboda shi Musulunci dukkansa kasa ne, mabiyansa su ne al’ummar Musulunci. Kuma al’ummar Musulmi ya wajaba Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW) su rika jagorantar su. Idan aka samu sabani a tsakanin Musulmi to Alkur’ani bai bar mu haka kawai ba: “Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaki, to, ku yi sulhu a tsakaninsu. Sai idan dayansu ta yi a kan gudar, to, sai ku yaki wadda ke yin zaluncin har ta koma zuwa ga umarnin Allah.” (Hujurati:9).
Wannan game da jama’a ke nan, hatta da mutum biyu za a samu fada da sabanin a tsakaninsu, babu makawa a warware ta hanyar tattaunawa, tattaunawa tana da muhimmanci domin mu kauce wa asara a tsakaninmu. Saboda lallai mu daga kowane gefe na Musulmi a lokacin da suke fada wani ya mutu, ko aka yi asarar wani abu, asara ce ta al’ummar Musulmi, kuma ba mu da waninta.
Allah Madaukaki Ya ce: “Kun kasance mafi alherin al’umma wadda aka fitar ga mutane, kuna umarni da alheri, kuma kuna hani daga abin da ake ki, kuma kuna imani da Allah. Kuma da Mutanen Littafi sun yi imani, lallai ne, da (haka) ya kasance mafi alheri a gare su. Daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawansu fasikai ne.” (Al-Imrana:110).
Allah Ya yi albarka a gare ni da ku cikin Alkur’ani Mai girma. Kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da Ambato Mai hikima. Lallai ne Shi, Madaukaki Mai yawan Kyauta ne Mai karimci, Mamallaki, Mai tausayawa Mai jinkai.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai