✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Musulmai na ci gaba da Allah-wadai da Indiya kan batanci ga Annabi

Masu kalaman dai mambobin jam'iyya mai mulkin kasar ne

Kungiyoyi da kasashen Musulmai da dama na ci gaba da yin Allah-wadai da kalaman batancin da wasu kusoshin jam’iyyar BJP mai mulki a Indiya suka yi ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Tuni dai wasu daga cikin kasashen suka fara yi wa jakadunsu da ke Indiyan kiranye, tare da kira ga kasar da ta nemi gafarar Musulmai kan lamarin.

A makon da ya gabata ne dai Nupur Sharma da Naveen Jindal, wadanda mambobin jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ne, suka yi kalaman batancin.

Sai dai daga bisani jam’iyyar ta sanar da dakatar da su daga cikinta, sannan ta ce ba ta goyon bayan cin zarafin kowanne addini.

Ita ma Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ake yi wa kallon kawa ga Indiyar ta yi Allah-wadai da kalaman na ’yan siyasar.

Kazalika, su ma kasashen Kuwait da Qatar da Saudiyya da Pakistan da ma sauran kasashen Musulmai su ma sun bi sahun Hadaddiyar Daular Larabawan.

Ita ma kasar Iran ta nuna takaicinta ta hanyar yi wa jakadanta da ke kasar kiranye, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar na IRNA ya rawaito.

Akalla dai kasashe 15, ciki har da Indonesia da Jordan da Libya da Maldives da kuma Oman ne suka fara shirya zanga-zanga a ofisoshin jakadancin indiya a kasashensu.

Ita ma Jami’ar Al-Azhar da ke kasar Masar, wacce daya ce daga cikin muhimman cibiyoyin Musulunci a duniya, ta bayyana kalaman a matsayin na ta’addancin da zai iya jefa duniya cikin rikici.

Kazalika, Kungiyar Hadin kan Musulmai ta OIC, ta ce kalaman sun kara fito da halin kuntatawar da ake yi wa Musulmai a Indiya.