An rantsar da Injiniya Mustafa Balarabe Shehu a matsayin sabon shugaban kungiyar Injiniyoyi ta Duniya da ake kira WFEO (World Federation of Engineering Organizations).
Tun a bara Injiniya M.B Shehu ya lashe zaben wanda Kungiyar Injiniyoyi da masu zayyana na reshen kasar Kosta Rika su ka gudanar wato Colegio Federado de Ingenieros y de Arquitectos de Costa Rica.
Ya karbi ragamar shugabancin WFEO a Prague, Jamhuriyar Czech yayin babban taron kungiyar da aka gudanar a Yammacin wannan Asabar.
Zai yi aiki a wannan matsayin na tsawon shekaru biyu (2023-2025) a birnin Paris na Faransa, inda sakatariyar WFEO take.
Injiniya Mustafa Shehu wanda dan asalin Jihar Kano ne, shi ne bakar fata kuma mutumin da ya fito daga yankin Sahara na farko da zai jagoranci kungiyar ta WFEO.
Kuma wannan ne karon farko da aka samu wani mutumin Sahara daga nahiyar Afirka da ya ɗare kan wannan kujera tun bayan kafuwar kungiyar shekaru 54 da suka gabata.
Kamar yadda WFEO ta bayyana a shafinta na X (Twitter), Mustafa Balarabe Shehu FNSE FAEng ya lashe zaben shugabancin WFEO da aka yi a watan Maris na 2022
Sanarwar da WFEO ta fitar a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris na 2022, ta tabbatar da nasarar Injiniya Shehu da cewa, “Muna taya Engr Mustafa B. Shehu dan Najeriya murna, wanda ya zama zababben shugaban kungiyar WFEO a taron da aka yi a San Jose, Costa Rica.
Babu shakka masu ruwa da tsaki da mahukunta sun tabbatar cewa WFEO ce babbar kungiyar Injiniyiyo ta Duniya mai zaman kanta.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Injiniya Shehu ya mika godiya ta musamman ga ’yan uwa da abokan arziki da suka taimaka masa da addu’o’i da goyon baya har ya cim ma wannan nasara.
Injiniya Shehu ya shugabanci Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya NSE reshen Jihar Kano daga 2000 zuwa 2022 da mataki na kasa daga shekarar 2012 zuwa 2013 da kungiyar Injiniyoyin Afirka daga 2015 zuwa 2016.
Kafin yanzu ya rike kujerar Mataimakin Shugaban WFEO.
Shehu ya yi aiki a wurare da-dama kafin ya bude kamfani na kansa, Amal Engineering Services wanda ya sauya sunansa zuwa Mustafa Balarabe Shehu Engineering Limited.
An dai haifi sabon shugaban na WFEO a ranar 12 ga watan Afrilun 1963.
Mujallar Abusites ta ce mahaifin Injiniyan wato Alhaji Shehu Salihu ya rasu ne a lokacin yana karamin yaro tun bai wuce shekaru 12 a duniya ba.
Sai dai mutuwar mahaifinsa ba ta hana shi ya ci gaba da gwagwarma a rayuwa ba, inda ya rika fadi-tashin da ya kai ga ya samu damar yin karatu har zuwa matakin zama injiniyan lantarki a Jami’ar ABU Zaria a 1985.
Ya soma karatun Firamare a garin Jahun da ke Jigawa, sannan ya tafi Sumaila kafin daga bisani ya koma Firamaren Kwalli da ke kwarywar birnin Kano.