Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 123 afuwa albarkacin Idin Karamar Sallah.
Gwamnan wanda ya kai ziyara gidan yarin da ke Goron Dutse a ranar Alhamis, ya ce wadanda aka yi wa afuwar an zabe su ne bisa irin girman laifinsu da kuma alamun halayya ta gari da suka nuna.
- Yadda sauran masu sallar Tahajjud 10 da aka sace a Katsina suka kubuta
- An soke bikin ranar samun ‘yancin kai a Kamaru
A cewarsa, wannan ziyara wata manuniya ce ga daurarrun domin su san cewa gwamnatin Jihar bata manta da su kuma tana ci gaba da daukarsu a matsayin al’ummar jihar.
Haka kuma ya ce, wannan wani yunkuri ne na yaba wa kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi don ganin an rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya Ambato Gwamnan yana shawartar fursunonin da aka yi wa afuwa da su dabi’antu da hallaya ta mutanen kirki sannan su yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa.
Kazalika, Ganduje ya bayar da Naira dubu biyar ga kowane daya daga cikin fursunonin da ya yi wa afuwa domin su samu kudin motar koma wa gidajensu.
A nasa jawabin, Kwanturolan Gidajen Yarin Kano, Suleiman Suleiman, ya yi wa Gwamnan godiya bisa ga wannan karamci na ’yantar da dubban fursunoni tun bayan hawansa kujerar gwamnatin jihar.
Suleiman ya shawarce su da suka kasance mutane ne na gari ta hanyar kauracewa aikata miyagun laifuka don gudun kada ‘Ungulu ta koma gidanta na Tsamiya’.
Baya ga haka, Ganduje ya kai ziyara gidan ladabtar da kananan yara da kuma na marayu a jihar Kano.