Malam Adamu Yakubu danzara, matashi ne mai karancin shekaru da ya shahara wajen gyaran babura. Maraya ne, wanda rashin mahaifansa ya sa ya ajiye karatunsa na sakandare domin ya tallafi kannensa guda uku, ta fuskar ciyar da su da kula da karatunsu. Wakilimmu ya sami zantawa da shi a bakin sana’arsa a yadin Dutse, inda ya yi masa karin bayanin rayuwarsa.
Da yake bayani, Malam Adamu ya ce wahala ta sa ya daina karatu saboda babu wanda zai dauki nauyin karatun ya kuma taimaka musu da abin da za su ci, shi da kannensa, lamarin da ya sa ya ajiye duk wasu harkokin rayuwa gefe ya rungumi sana’ar gyaran babura don ya rike kannen nasa sakamakon mutuwar mahaifansu.
Adamu ya kara da cewar da sana’ar ce yake ciyar da kannensa, yake biyan kudin karatunsu, yake kuma kula da lafiyarsu, idan bukatar hakan ta taso. A kan haka, ya ce babu abin da zai ce wa Allah sai godiya, domin Ya sa albarka a cikin sana’ar tasa, domin bayan daukar dawainiyar kannen nasa, “Wasu kan rabu da ni su sami alheri, musamman ma wadanda nake gwada musu gyaran baburan kuma da yawa sun amfana ta wannan hanya, su tafi suna dogaro da kansu.” Inji shi.
A daidai wannan gaba ce ya bukaci shugaban karamar Hukumar Dutse da ma gwamnatin Jihar Jigawa da su taimaka masa da jari, wanda zai sayi kayan aiki irin na zamani domin ya bunkasa sana’arsa.
Haka nan ya kara da cewar akwai bukatar gwamnatin jihar ta Jigawa ta taimaka musu wajen daukar nauyin karatun iri-irinsa a matsayinsu na marayu, musamman da yake ya sami labarin gwamnatin tare da wata kungiya a karkashin Hajiya Ladi Gwaram suna taimaka wa marayu da marasa galihu. “Lallai muna son gwamnati ta tallafa mana a kan sana’o’inmu, don mu dogara da kanmu.”
Ya nuna damuwarsa game da maraici da yake damunsa, musamman saboda karancin shekaru da yake da shi, idan aka yi la’akari da irin halin rayuwar da ake fuskanta a halin yanzu. Sannan ya bukaci jama’a da kungiyoyin bayar da tallafi ga marasa gata da ke ciki da wajen Jihar Jigawa su kara kaimi wajen taimaka wa irinsa wajen inganta sana’arsu kowace iri ce. Musamman ma dai shi ya yi nunin cewa in ya sami tallafi kan sana’arsa ta gyaran babura, zai iya dogara da kansa kuma ya iya daukar nauyin kansa wajen kammala karatunsa da shi da sauran ’yan uwansa da aka mutu aka bar su.
Muna son gwamnatin Jigawa ta taimaka mana kan sana’o’inmu -Adamu danzara Daladanci
Malam Adamu Yakubu danzara, matashi ne mai karancin shekaru da ya shahara wajen gyaran babura. Maraya ne, wanda rashin mahaifansa ya sa ya ajiye karatunsa…