Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif ya ce ya zama wajibi jiga-jigan APC su yi aiki tukuru muddin suna son ganin mafarkinsu na shafe shekara 50 tana mulki a Najeriya ya zama gaskiya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
- Rashin man fetur ya sa ’yan bindiga sun koma amfani da rakuma a Sakkwato
- Sarkin Gombe zai nada Gwamna Inuwa Yahaya sarauta
Sanata Ali Modu, wanda daya ne daga cikin masu zawarcin Shugabancin jam’iyyar a matakin kasa ya ce dole sai sun yi aiki tukuru wajen ganin APC ta ci gaba da mulki bayan karewar wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.
Tuni dai tsofaffin Gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka fara zawarcin shugabancin kujerar, duk da cewar jami’iyyar ba ta kammala yanke shawara kan shiyyar da za ta kai kujerar ba.
Sanata Sheriff ya ce, “Yau, a matsayinmu na jam’iyya, shekararmu shida kacal a kan karagar mulki, babban burinmu shi ne APC ta shafe shekara 50 tana mulkin Najeriya.
“Shi Buhari ne ya kawo wannan maganar, kuma ina makomarta za ta kasance bayan kammala wa’adinsa? Shin mun shirya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa za mu iya daukar nauyinsu?
“Matukar muna son yin haka, to tilas mu rungumi kowa da kowa. Kana bukatar wadanda suka san tarihin jam’iyyar da ma na kasar, wadanda suka yi gwagwarmayar rayuwa domin kai Najeriya ga tudun mun tsira.
“Yin hakan amma fa ba abu ba ne mai sauki, dole sai mun tashi tsaye mun yi aiki. Saboda haka ya zama wajibi na tuntubi dukkan ’yan jam’iyyarmu, mata da matasa daga bangarori daban-daban wajen ganin APC ta ci gaba da mulki nan da shekara 30 ko 40 ko ma 50 masu zuwa da yardar Allah,” inji Sanata Ali Sheriff.