✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Muna neman taimakon Indiya don fitar da mutane daga talauci’

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya nemi kasar Indiya ta taimaka a yunkurinta Najeriya na fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekara…

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya nemi kasar Indiya ta taimaka a yunkurinta Najeriya na fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekara 10.

Lawan ya yi kiran ne yayin karbar bakuncin Jakadan Indiya a Najeriya, Abhay Thakur, a ofishinsa a ranar Litinin a Abuja.

“Indiya ta yi kokari wajen kawar da talauci a kasarta saboda haka za mu ji dadi idan kuka taimaka mana da hanyoyin da kuka bi don ganin mun kawar da talaucin cikin sauri da inganci.

“Idan za ka cire mutum miliyan 100 daga kangin talauci dole ne sai kana da tsari da ma’aikatu da za a yi amfani da su wajen cimma manufar, kuma muna da zummar yin hakan”, inji shi.

Shugaban Majalisar ya kuma jinjina wa kasar ta Indiya bisa kokarin da ta yi na ba jami’an tsaron Najeriya horo kan yaki da ta’addanci.