Amurka ta gargadi China game da yunkurin taimaka wa Rasha a yakin da take yi da Ukraine, matukar ba haka ba kuma za ta dandana kudarta.
Bayanai daga Amurka na cewa ta karkashin kasa Rasha ta nemi tallafin karin sojoji da kayayyakin yaki, kuma China na duba yiwuwar taimaka mata, abin da a cewar Amurka zai kara tsananta yakin.
- Zan tsaya takarar Gwamnan Kaduna – Sanata Uba Sani
- ’Yan bindiga sun farmaki ’yan kasuwar albasa a Sakkwato
Sai dai kuma tuni Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta musanta zargin, inda ta ke cewa da gayya Amurka ta bullo da wannan zancen don kawai jefa ta cikin rikicin da gangan.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa ta musamman da aka yi a tsakanin ministocin kasashen wajen Amurka da China a birnin Rome.
A yanzu haka dai bayanai na cewa za a koma ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin kasashen Ukraine da Rasha karo na Hudu a ranar Talata.
A cewar guda daga cikin tawagar Ukraine a tattaunawa da Rasha, Mikhailo Podolyak ta cikin wata wallafar shafin Twitter, ya ce yana fatan a wannan karo za a cim ma matsaya.