’Yan bindiga sun saki wani bidiyo suna ikirarin cewa suna da buhu-buhun sabin Naira da aka sauya wa fasali da suke sayen makamai da su.
A bidiyon da ke yawo kafofin sada zumunta, an ji ’yan ta’addan da ke rike da sabbin kudaden suna ikirarin cewa tuni suka fara harkokinsu na ta’addanci da sabbin takardun kudin.
- CBN ya boye sabbin takardun Naira —Gwamnan Jigawa
- Har yanzu ban taba ganin sabbin takardun Naira ba —Gwamna Ortom
“Wani ma da ake nufi bai samu sabbin kudin ba, amma sun zo hannunmu,” in ji mai magana da yawunsu.
Ya ce buhunan sabbin kudaden, “Da ke gare mu, Allah Kadai Ya san iyakansu… har mun sayi makamai da su.”
A gefe kuma aka ji wani na cewa,“Ina da miliyan goma (na sabbin kudaden a) gida.”
Aminiya ba ta iya tantance gaskiyar ikirarin ’yan ta’addar ba ko kuma lokacin aka dauki bidiyon.
Amma wannan na zuwa ne duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gurgunta tattalin arzikin ’yan ta’adda na daga cikin manyan dalilanta na sabunta fasalin takardun kudin.
A halin yanzu dai ’yan Najeriya na fama da karancin sabbin takardun kudin, duk kuwa da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara wa’adin amfani da tsoffin kudin da kwana 10.
Aminiya ta ruwaito Gwmanan Jihar Jigawa, Abubakar Muhammad Badaru, na zargin CBN da boye sabbin takardun kudin a jiharsa, ya ki ba bankuna isassu da za su koda a ATM.
Rahotanni sun nuna a halin da ake ciki, hatta takardun tsoffin kudin na kamshin turaren dan goma a wurin ’yan Najeriya.
Sakamakon haka, masu harkar cirar kudi ta POS na cin karensu babu babbaka wajen tsawwala cajin da suke yi wa kwastomomi, a wani wuri har cajin kashi 30 cikin 100 na kudin da kwsatoma ke bukata suke karba.
Wannan na da nasaba da karancin sabbin takardun kudin a bankuna, inda dubban daruruwan ’yan Najeriya ke kwashe awanni suna bin layi ba tare da sun samu ba.
Rahotannin baya-bayan nan sun nuna a wasu bankuna ko mutum daya ba a samu a cikin zaurukan ajiyar kudi.
Wasu kuma ke kayyade ba wa kwastamomi Naira 5,000 zuwa 10,000 na kudaden leda (N5, N10, N20, ko N50) wadanda ba su da farin jini.