Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a asibitocin gwamnatin Najeriya sun dage kan karin albashi na kashi 200.
Kungiyar ta National Association of Resident Doctors (NARD), ta bayyana haka ne makonni biyu bayan janye yajin aikin gargadi na yini biyar da suka yi domin jiran gwamnati ta yi wani abu kan bukatunsu.
- Hajji: Sarkin Zazzau ya gargadi maniyyata kan zuwa da goro Saudiyya
- Yadda ’yan bindiga sun kashe mutum 62 a Zamfara da Sakkwato
Cikin wata sanarwa, kungiyar ta ce ba za ta amince da karin albashi na kashi 35 cikin 100 da gwamnatin da ta shude ta yi ba sannan kuma sauran bukatunsu har yanzu ba a yi komai a kai ba.
Janye wani kudiri da ke neman hana likitocin da suka kammala karatu a baya-bayan nan ficewa daga kasar har sai sun yi aikin shekara biyar, da diban likitoci aiki domin maye kwararrun da suka daina aiki da kuma gaggauta inganta asibitocin gwamnati wasu ne daga cikin bukatun kungiyar.
Likitocin na son Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta warware matsalolinsu ya kuma aiwatar da matakan rage wa ’yan Najeriya radadin janye tallafin mai.
Shugaban kungiyar, Dokta Emeka Orji ya bukaci sabuwar gwamnati da ta fifita batun barin kasar da likitoci suke yi.
Akwai likitoci 10,000 da ke aiki a asibitocin gwamnati zuwa Nuwamban bara, sai dai rashin albashi mai kyau da karancin kayan aiki da kuma rashin walwalar ma’aikatan lafiya ya sa kwararru a bangaren lafiya na neman wasu damarmakin a kasashen waje.