✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna buƙatar Dala biliyan 10 a riƙa samun wutar sa’o’i 24 a Najeriya — Ministan Lantarki

Dole sai abokan hulɗa masu zaman kansu sun zuba jari a ɓangaren makamashi domin lamarin ya fi ƙarfin gwamnati.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana buƙatar zuba jari na Dala biliyan 10 a ɓangaren makamashi nan da shekaru biyar zuwa goma masu zuwa domin a riƙa samun wutar lantarki ta sa’o’i 24 a ƙasar.

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan yayin karɓar baƙuncin Darekta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Gine-Gine ta ICRC, Dokta Jobson Ewalefoh.

A cewar Ministan, a halin yanzu Gwamnatin Nijeriya ita kaɗai ba za ta iya zuba jari na Dala biliyan 10 ba a ɓangaren makamashi alhali akwai wasu ɓangarorin masu muhimmanci da ke buƙatar kulawa.

Ya ce a dalilin haka ne gwamnatin ke neman abokan hulɗa masu zaman kansu domin zuba jarin da zai tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen inganta wutar lantarki a faɗin ƙasar.

A bayan nan dai matsalar wutar lantarki na ci gaba da ta’azzara a faɗin Najeriya musamman a Arewacin ƙasar inda a makonni bayan nan aka aƙalla kwanaki 10 ana zaune cikin duhu.

Mahukunta dai na ci gaba da ta’allaka lamarin da tangarɗa a manyan layukan samar da wutar lantarkin da kuma hare-haren da ’yan ta’adda ke kaiwa da zummar lalata wutar.