✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna aiki ba dare ba rana domin ceto ɗaliban Kuriga — Gwamnatin Kaduna

Yau mako ɗaya ke nan da ’yan bindiga suka sace ɗalibai 287 a ƙauyen Kuriga da Jihar Kaduna.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce tana aiki ba dare ba rana domin ganin an dawo da dukkan ɗaliban makarantar garin Kuriga lafiya.

Kwamishinar Kula da Ayyukan Jin ƙai da ci gaban jama’a, Hajiya Rabi Salisu ce ta ba da wannan tabbacin a yayin wani tattaki na zaman lafiya albarkacin Ranar Mata ta Duniya da Gidauniyar CLEEN ta shirya.

Ta ce, “Muna goyon bayan abin da kuke yi, ɗalibai 287 da aka sace za a dawo da su gida. Gwamna Uba Sani yana aiki ba dare ba rana, duk za a dawo ɗaliban.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, ’yan bindiga suka far wa makarantar Firamare da Sakandiren ƙauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna inda suka sace daliban su 287.

A halin da ake ciki, Gidauniyar CLEEN da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana aniyarsu ta ciyar da harkokin matan Najeriya gaba, musamman manufofin da suka dace da jinsi, da inganta rayuwar al’umma da bai wa kowa ‘yanci.

Sun bayyana hakan a wani taron horaswa na kwanaki biyu, mai taken, ‘Tattaunawar Siyasa kan Tsare-tsare da Ayyuka na Jiha kan jinsi’ wanda Gidauniyar CLEEN tare da haɗin gwiwar Ofishin Jakadancin Norway da Mata na Majalisar Ɗinkin Duniya suka shirya a Kaduna.