Hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, ta yi asarar jami’anta 16 yayin wani artabu da suka yi da barayin shanu a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar ranar Alhamis da ta gaba ta.
An kuma ceto jami’an hukumar 20 da suka bace. Kamar yadda kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya sanar.
Shehu, ya ce, a yanzu haka an tanadi jami’an tsaron hukumar na musamman da jami’an mobayil tare jiragen sama don bankado maboyar barayin shanun da ke yankunan jihar.