✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun soma aikin gyara lalacewar wutar lantarki a Arewa — TCN

Babu takamaiman lokacin dawo da wutar lantarki da aka ɗauke a sassan yankin Arewa.

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Nijeriya (TCN) ya ce ya soma aikin gyara a layin tasharsa da ya gano ya samu matsala, wanda ya yi sanadiyar katsewar wuta a wasu sassan ƙasar.

Lamarin wanda ya auku ne tun daga ranar Litinin 21 ga watan Oktoba kana ya shafi yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan yankin Arewa ta tsakiya a Nijeriya inda duk suka kasance cikin duhu.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar sashin hulda da jama’a na Kamfanin TCN, Ndidi Mbah ta ce, tun daga ranar da aka samu katsewar wutar, tawagar ma’aikatan kamfanin suke ta koƙarin neman inda matsalar take amma ba su yi “nasara ba” sai a yammacin ranar Laraba.

“Layin wutar da ya samu matsala ya kai tsawon inch 9, kuma ƙarfinsa ya kai Kilowatt 330 wanda ke hanyar tashar wuta a fadamar dajin Igumale da ke Jihar Benuwe,” a cewar sanarwar da Kamfanin TCN ya wallafa a shafinsa na X.

“Bayan gano inda matsalar take, a yammacin ranar Laraba, tuni aka soma shirye-shiryen aika kayayyakin aiki zuwa wurin da lamarin ya faru don bai wa TCN damar fara ayyukan gyara,” a cewar sanarwar.

“Sakamakon yanayin wurin da matsalar ta faru, TCN na buƙatar aika manyan motocin tono da ɗibar yashi da sauran kayan aiki daga ofishinsa na yankin Enugu zuwa inda lamarin ya faru domin soma aikin gyara,” kamar yadda sanarwar ta yi kari a kai.

Sai dai Aminiya ta ruwaito TCN yana cewa babu takamaiman lokacin dawo da wutar lantarki da aka ɗauke a sassan yankin Arewa.

TCN ya ce duk da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar, amma matsalar rashin tsaro ta sa ba za a iya ci gaba da aikin gyaran ba.

Babbar jami’ar TCN, Nafisatu Asabe Ali, ta ce kamfanin ya samu takardar gargaɗi daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro cewa akwai haɗarin gaske shiga yankin da aka lalata manyan turakun lantarki uku, saboda matsalar rashin tsaro.

A cewarta, duk da cewa kamfanin ya riga ya tanadi kayan aikin gyaran, amma ba zai iya shiga wajen ba, sai ya ki daga hukumomin tsaro.

Kimanin kwanan huɗu a jere ke nan da aka ɗauke wutar bayan lalacewar babban layin lantarkin Shiroro zuwa Manzo, wanda ke isar da wutar ga akasarin yankin Arewa.

Bayan lalacewar layin ne TCN ya yi ƙoƙarin amfani da layin Ugwaji zuwa Apir mai ƙarfin 330kV domin tura wuta zuwa yankin, amma aka yi rashin sa’a shi ma ya lalace.

TCN ya bayyana cewa matsalar ta jefa jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da wani yanki na Arewa ta Tsakiya cikin duhu.

Injiniya Nafisa ta bayyana cewa har yanzu babban layin Shiroro ba ya aiki, kuma ba za a iya cewa ga takamaiman lokacin da za a gyara shi ba saboda matsalar tsaro.

Ta ci gaba da cewa ko da an gyara layin Ugwaji zuwa Apir mai ƙarfin 750kV, ƙarfin wutar da zai iya ɗauka a yanzu bai wuce 350kV.

Don haka sai dai a ba wa wasu yankunan jihohin Kano da Kaduna da Jamhuriyar Nijar.