Sashen Binciken Lafiyar Ababen Hawa (VIO) na Babban Birnin Tarayya Abuja ya ce ya ragargaza babura 3,200 da aka kwace daga hannun ’yan acaba daga watan Nuwamban 2021 zuwa watan Yulin 2022.
Sashen ya kuma ce yanzu haka akwai babura kimanin 600 da suke jiran umarnin kotu su ma su lalata su.
Kakakin VIO shiyyar birnin, Kalu Emetu ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce VIO ta fara kwacen ne domin hana sana’ar acaba a kwaryar birnin Abuja.
Sai dai ya ce a kodayaushe sukan sami izinin kotu kafin su ragargaza baburan.
“Idan muka tara babura da yawa, mukan je kotu mu sami izinin lalata su. Idan muka kammala lalatawar kuma, mukan sayar da karafan ga kamfanonin da za su yi amfani da su.
“Irin wadannan kamfanonin kan yi amfani da su wajen sarrafa wasu abubuwan, yayin da kudin kuma ake zuba su a lalitar Gwamnatin Tarayya domin ta yi amfani da su,” inji Kakakin na VIO.