Shugaban Kungiyar Mata Masu Da’awa (Women In Da’awa) ta Kasa, Hajiya Maryam Idris Usman ta ce sun musuluntar da mata 800 a Karamar Hukumar Rijau da ke Jihar Neja. |
Shugabar ta bayyana haka ne a wajen babban taron kungiyar na kasa da suka gudanar a Bauchi a karshen makon jiya, inda ta ce yanzu haka suna gina manyan masalatai a cikin gidajen yari na Nasarawa da Keffi a Jihar Nasarawa.
Hajiya Maryam Usman ta ce, “A Jihar Adamawa kuma, mun samar wa yara marayu da marasa galihu su 100 guraben karatu, domin su samu ilimi yadda ya kamata. Sannan muna gina makarantar marayu da marasa galihu yanzu haka a nan Jihar Bauchi. Aikin gina makarantar da muke yi a garin Tilden Fulani sama da shekara biyar mun gagara kammalawa, don haka muna neman goyon baya da tallafin gwamnatin Jihar Bauchi domin kammala aikin.”
Shugaban ta ce ayyukansu sun hada da fadakarwa da ilimantarwa da tallafa wa gajiyayyu da marasa karfi, sai ta roki gwamnatoci da masu hannu da shuni su rika taimaka wa kungiyar domin gudanar da ayyukan alherin da take yi ga jama’a da ci gaban addinin Musulunci.
Hajiya Maryam, ta ce wasu daga cikin ayyukan suna yi ne in suka samu zakka da sadakoki daga hannun daidaikun mutane.
A jawabin Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, wadda Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Khadija Mohammed Abdullahi ta wakilta ta ce tun zuwanta wannan matsayin take da shirye-shirye na musamman domin inganta rayuwar mata da ci gabansu.
Hajiya A’isha Buhari, ta ce tana da shirye-shirye na musamman domin inganta rayuwar matan Najeriya, sai ta yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin mata suna samun kyakkyawan yanayin rayuwa, inda ta yaba wa ayyukan da mata masu da’awar suke gudanarwa.
A jawabin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, wanda Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilawanu Sulaiman Adamu ya wakilta ya ce halin da ake ciki mata suna samun kwarin gwiwa sosai wajen neman ilimi sakamakon fadakarwa da ilimantar da su da ake yi.
Ya ce “A shekarun baya matanmu ba su zuwa makaranta domin neman ilimi, amma a yanzu an samu karuwa sosai ta fuskan halartar makarantun mata domin neman ilimin addini da na zamani, hakan ya sa an samu ci gaba sosai ta fuskar fahimtar addinin Musulunci da abubuwan da Musuluncin ya zo da su.”
Sai ya shawarci matan su dage domin su samu nasarar cimma abubuwan alherin da suke yi.