Shugabar Gidauniyar Inganta Rayuwar Mata da Yara, ta Kwatam Women and Children’s Empowerment Initiatibe, Malama Tabitha Ari Mai Sule, ta ce sun koya wa mata da yara sama da dubu daya sana’o’i cikin shekara biyu da kafa gidauniyar a kokarinsu na ganin yara kananan suna samun shiga makarantu don dogaro da kansu.
Malama Tabitha Ari Mai Sule, ta ce cikin shekara biyu bisa jajircewarsu da taimakon wadansu kusoshin gwamnati ne suka koya wa mata fiye da 1,000 sana’o’in hannu da suka hada da saka da yin takalma da jakunkunan mata da sabulu da man shafawa da gyaran gashi da dinki da sauransu.
A cewarta, bayan sun koya musu sana’o’in sukan tallafa musu da jari na Naira dubu 10, don su fara sana’ar da aka koya musu.
Shugabar Gidauniyar ta ce, kyauta suke koya musu sana’o’in na tsawon wata uku bayan sun sayi fom Naira 500, daga nan ba za su sake biyan ko kwabo ba, sai lokacin da suka gama sai a ba su kayan koyon sana’a da jarin Naira dubu 10.
Malama Tabitha Ari, ta ce a kwanan nan, sun sake koya wa wadansu mata 560 sana’o’i daban-daban da suka samu tallafin Naira dubu 10 kowacensu.
“Wanda ta koyi dinki ita ba Naira dubu 10 muke ba ta ba, saboda keken dinki yana da tsada; mukan samar musu da keke ne da tallafin Mataimakin Gwamnan Jihar Borno na yanzu wanda a lokacin yake Shugaban Karamar Hukumar Biu, inda ni kuma nake matsayin mai ba shi shawara kan harkokin mata, shi kuma dan majalisarmu na tarayya, Aliyu Betara, ya ke ba da tallafin Naira dubu goma-goma,” inji ta.
Ta shawarci matan da suka ci gajiyar koyon sana’ar su ririta abin da suka samu don su dogara da kansu su tallafi iyalansu, musamman matan da mazansu suka rasu a rikicin Boko Haram.
Ta ce burin Gidauniyar Kwatam Women and Children’s Empowerment Initiatibe, shi ne mata sun dogara da kansu su da yaransu.
Ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Borno ta kara kula da harkar mata da marasa galihu wajen ba su tallafi domin kawar da hankalinsu daga tunanin aikata wani mugun aiki.
Wadansu daga cikin matan da suka koyi sana’o’in, sun gode wa gidauniyar kan yadda ta koya musu sana’o’in don dogaro da kai.