A ranar Juma’ar da ta gabata ce Hukumar Ahmadu Bello da ke Zariya ta gudanar da bikin gwajin motocin da ta kera a harabar jami’ar da ke Samaru, inda a ranar Litinin aka wuce da motocin garin Legas don kai su kasar Netherlands, kasar da za a gudanar da gasar tseren motocin.
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kera motocin ne domin shiga gasar tseren motoci na duniya da za a yi a kasar Netherlands a ranar 13 ga Mayu shekara ta 2015.
Bayan kammala bikin ne wakilin Aminiya ya tattauna da Dakta Muhammadu Dauda Shugaban sashin kere-kere na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin jin hanyar da suka bi har suka samu nasarar kera motocin. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Za mu fara da tarihinka a takaice?
Dakta Dauda: Assalamu alaikum, to da farko sunana Dakta Muhammadu Dauda kuma ni ne shugaban sashin tsara taswira da kere-kere na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma ni mutumin Potiskum ne da ke Jihar Yobe. A yanzu ina da kimanin shekara 47. Na yi makarantar firamare har zuwa sakandare a jihata, wato Yobe ke nan, sannan na yi digirina na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Bayan na yi digiri ne Jami’ar Ahmadu Bello ta ba ni aiki a wannan tsangayar ta kere-kere, kuma na fara karatun digiri na biyu a nan, daga bisani na yi digiri na uku a Ingila. Bayan na dawo gida Najeriya ne na ci gaba da aiki a wannan sashi har Allah Ya sa na zama shugabansa.
Aminiya: Wacce hanya kuka bi har kuka kera wadannan motoci?
Dakta Dauda: Game da hanyoyin da muka bi har muka kera motocin nan kuwa, a gaskiya Kamfanin Mai na Shell ne ya bukaci daliban wadansu jami’o’in kasar nan su shiga gasar kera motocin tsere na duniya da za a gudanar a wannan shekarar, musamman ma a kasashen da suka ci gaba dalibai ne ke kera irin wadannan motocin, don haka sai kamfanin ya zabi jami’o’i biyu, wato Jami’ar Benin da kuma Jami’ar Legas, su kuma wadannan jami’o’i sai suka bada shawarar cewa a sanya Jami’ar Ahmadu Bello, daga cikin masu gudanar da gasar sun sani cewar muna da kwararrun ma’aikata da kuma dalibai, sannan muna da sashi na musamman da zai iya zana taswirar motoci da kuma kera su, don haka Kamfanin mai na shell ya shawarce mu ko za mu iya muka amsa mata cewa, eh za mu iya, kuma ga shi Allah Ya taimake mu mun yi nasara.
Na farko abin da muka yi shi ne, akwai wadansu ayyukan da daliban da suke zangon karatunsu na karshe ke yi, wanda ake kira project, sai muka ce idan wadannan daliban suka yi wannan aikin to zai jawo musu bajinta, a lokacin project sukan yi abubuwan bajinta, sannan abu na biyu shi ne, sai muka fara tsara taswirar motar, wato zane kafin muka dauka zuwa dakin kerawa, domin ba zai yiwu ka kera abu ba tare da zana taswirarsa ba.
Aminiya: Ta wace hanya kuka bi kuka samo kayayyakin da kuka kera wadannan motocin?
Dakta Dauda: Da farko kayayyakin da aka kera wadannan motocin kusan kashi 70 cikin 100 a Najeriya suke, kuma kusan mafi yawansu duk a nan Zariya muka samo su, kadan ne daga ciki ne muka samo Fanteka da ke Kaduna, mafi yawan karafan da muka yi amfani da su a Ajakuta aka yi su, kuma wayoyin motocin na tsofaffin kwamfitoci ne, sai muka harhada muka yi amfani da su wajen kera motocin. Abu na biyu shi ne, mun yi amfani da injin din babur, wanda ake kira roba-roba a matsayin injin motocin, da shi muka yi amfani illa kawai mun kara masa wasu abubuwa ne domin ya kara karfi, ya kuma rage shan mai, sai kuma katako irin na roba da shi muka yi cikin motar, muka kuma inganta shi har ma ya fi na motocin da ake shigo mana da su inganci da kyau.
Aminiya: Ita wannan motar nauyinta zai kai kilo nawa?
Dakta Dauda: Nauyinta zai kai akalla nauyin kilo-giram 200, dama daga cikin ka’idojin kera mota ba a so nauyinta ya wuce kimanin nauyin kilo-giram 210, namu kuma sun tsaya a kilo giram 200 daidai.
Aminiya: Kimanin Naira nawa kuka kashe wajen kera wadannan motocin?
Dakta Dauda: To akalla mun kashe kimanin Dala dubu 20, kwatankwacin kudin Najeriya Naira miliyan 3 ke nan, domin ka san wannan shi ne karo na farko da muka kera mota, don haka dole su yi tsada, amma nan gaba idan muka ci gaba da kwatanta basirarmu motocin za su dawo kasa da Naira dubu 150.
Aminiya: Ku dauki kwanaki nawa wajen kera wadannan motocin?
Dakta Dauda: Kusan wata shida, ka san wannan shi ne karo na farko, idan za mu kera nan gaba ba lokacin ba zai kai haka ba.
Aminiya: Kana jin za ku iya cin gasar tsaren da za a gudanar a kasar Netherlands?
Dakta Dauda: kwarai kuwa muna da kwarin gwiwa, domin kai kanka ka ga yadda aka gwada motocin da kuma irin tafiyar da suka yi, abu na farko da zai ba ka sha’awa shi ne motocin ba su da shan mai sosai, kuma nauyinsu ya yi daidai da irin yadda ake so, wannan shi ya sa muke alfaharin cewar idan muka shiga wannan gasar za mu yi nasara, kuma yanzu haka maganar da muke yi da kai motocin sun tafi Legas tare da wasu daga cikin daliban da muka kera motar tare, ni ma zan bi su domin kamfanin mai na Shell shi ne zai zabi daya daga cikin jami’o’in uku da na fada maka, wato tsakanin Jami’ar Benin da Jami’ar Legas sai kuma Jami’ar Ahmadu Bello, kuma na san Insha Allah a cikin ukun nan mu ne za mu yi na farko.