✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda

Uku daga cikin matasan da ke hannu ’yan asalin Jihar Katsina ne sai kuma wani ɗaya daga unguwar Hotoro da ke Kano.

Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris.

SP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47.

Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da wuƙaƙe da adduna da wayoyin hannu da wasu layu.

Ya bayar da sunayen matasan da ke hannu da suka haɗa da — Shukurana Salihu mai shekaru 25 da Rabi’u Dahiru mai shekaru 35 da Ya’u Idris mai shekaru 30 duk daga Jihar Katsina sai kuma Muktar Sani mai shekaru 30 daga yankin ’Yandodo na unguwar Hotoro da ke Kano.

SP Kiyawa ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan ababen zargin da ke tsare a sashen binciken miyagun laifuka na hedikwatarsu da ke Bompoi.

Rundunar ’yan sandan wadda ta ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike, ta kuma jaddada ƙudirinta na kawo ƙarshen duk wasu miyagu a faɗin jihar.

Ta kuma miƙa godiya ga al’umma dangane da goyon baya da haɗin kan da take samu a ƙoƙarinta na yaƙi da masu tayar da zaune tsaye.

Kayayyakin da aka kama a hannun ababen zargin Hoto: SP Abdullahi Haruna Kiyawa