Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce ta gano akalla mutum 29,000 da suka yi katin zabe fiye da sau daya a Jihar Kwara.
Kwamishinan Zabe na Jihar, Malam Garba Attahiru ne ya bayyana hakan a wajen taron bikin Ranar Dimokuradiya ta Najeriya, wanda makaranatar Micheal Imoudu Institute for Labor studies (MINILS) ta shirya.
- Mutanen gari sun babbake ‘barawon babur’ a Bauchi
- Isra’ila ta harba makami mai linzami filin jirgin saman Syria
Ya kuma ce kaso 50 cikin 100 na wadanda suka yi rajistar tsakanin watan Yuni zuwa Disamba sun maimaita ne.
Kazalika ya ce yana da kyau al’umma su sani hukuncin wannan laifin shi ne daurin gidan kaso na shekara guda ko tarar Naira miliyan daya, ko kuma duka biyun.
A nasa bangaren Shugaban makaranatar, Kwamared Issa Aremu, ya yi godiga ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa kafa tarihin da ya yi na ayyana ranar Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya din tunawa da ranar da aka soke zaben Shugaban Kasa a shekarar 1993.