Hukumar Tsaro ta DSS ta ce ta kama kayayyakin da suka hada da kakin sojoji da kudaden kasashen waje da dama a gidan Tukur Mamu, dan jaridar nan da ke shiga tsakani da ’yan bindiga.
Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci a kan sakamakon binciken da suka yi a gidan mawallafin jaridar nan ta Desert Herald da sanyin safiyar Alhamis.
- Sarauniyar ingila ta rasu tana da shekara 96
- Kidayar 2023: Za mu kashe N21bn don shata taswirar Najeriya – Osinbajo
DSS ta kuma ce ta kama abubuwa da dama a gidan, kuma da zarar ta kammala bincike za ta maka shi a agaban kotu.
A cewar Afunanya, “Yanzu haka, jami’an tsaron sun samu izinin bincike gidansa da ofishinsa, kuma a nan ne aka sami irin wadannan kayayyakin.
“Sauran kayayyakin sun hada da kudaden kasashen waje daban-daban da abubuwan hada-hadar kudi.
“Yayin da muke ci gaba da bincike, tabbas za mu gurfanar da shi a gaban kuliya,” inji Kakakin na DSS.
A ranar Laraba ce dai hukumar ta cafke Tukur Mamu a filin jirgin sama na Kano, bayan ta sa an tiso mata keyarshi daga kasar Masar.