Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci.
Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa.
A cikin bukatar da Mamu ya gabatar a jiya Litinin 30 ga watan Mayu, ya nemi a bayar da belinsa dsaboda yanayin rashin lafiyarsa.
Ya nemi Gwamnatin Tarayya ta ba shi izini a kai shi asibiti don yin aikin tiyata kamar yadda likitoci a kasar Masar da na Najeriya suka ba da shawarar.
Tun a ranar 21 ga Maris na shekarar 2023 ne dai gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mamu a gaban kuliya bisa zarginsa da taimakawa ta’addanci a kasar nan.
Ana masa tuhume-tuhume guda 10 da ke da alaka da ta’addanci amma ya musanta duka zarge-zargen.