Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwarsa kan mawuyacin halin da ya ce hambararren Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum na ciki.
Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Farhan Haq, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin New York na Amurka, ranar Alhamis.
- ‘Farashin gas din girki zai iya tashi a Najeriya mako mai zuwa’
- ECOWAS ta umarci dakarunta su dauki matakin soji a kan Nijar
Bazoum dai ya koka cewa a wajen da yake ajiye a hannun sojoji yanzu, ko lantarki babu, sannan babu ingantaccen abinci da magunguna.
A cewar Farhan, “Sakatare-Janar na nuna matukar damuwarsa kan lafiya da kuma tsaron da Shugaban Kasa da iyalansa ke ciki, sannan tana sake kiran a gaggauta sakinsa ba tare da wani sharadi ba, sannan a mayar da shi kan kujerarsa.
Antonio ya kuma yi koken cewa akwai rahotannin ci gaba da kamawa tare da tsare jami’an gwamnatin Bazoum, inda su ma ya bukaci a gaggauta sakin su.
Sakatare-Janar din ya kuma ce majalisar na goyon bayan kokarin shiga tsakanin da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) wajen dawo da Kundin Tsarin Mulki ya ci gaba da aiki a kasar.
Idan za a iya tunawa, da yammacin Alhamis ECOWAS ta umarci dakarunta da su daukin matakin soja wajen ganin an dawo da mulkin farar hula a kasar.